Tarukan karawa juna sani da horaswa dangane da amfani da bayanai a aikin jarida

Tarukan karawa juna sani da horaswa dangane da amfani da bayanai a aikin Jarida

Akwai mai neman hanyoyin inganta illimi a fannin alakluma da lissafi? Wadannan shafukan suna koyar da jama’a kyauta ko kuma a farashi mai rahusa. Kuma akwai darussan a hotunan bidiyo dangane da batutuwa daban-daban da harsuna ma haka.

Kuna iya duba shafin GIJN a Youtube domin samun irin wadannan darussan kyauta.

Code Academy/Makarantar Code  Wannan na bayar da darussa kyauta da kuma farashi mai rahusa a darussan da suka hada da Python, SQL, PHP, C++, R, Java da sauransu. Akwai kuma zabin kasancewa mamba inda za’a rika biyan $20/wata-wata amma za’a dauka kudin shekara guda a tashi daya. Da wannan kudin mutun zai ci moriyar samun kwasa-kwasai daban-daban.

Cousera na bayar da darussa kyauta, ga wadanda kuma ke neman kwarewa ta musamman a wasu fannonin (Mutun na iya biyan $49/Kowace wata) a kimiyyar bayanai, alkaluma da kuma fasahohin shirye-shirye ko kuma programming language daban-daban a jami’o’i daga kusan duk kaasashen duniya. Ana gabatar da darussan a harsunan da suka hada da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci, Jamusanci da wasu da dama.

Datawrapper: Kayayyakin gudanar da taron karawa juna sani.

edX na bayar da darussa kyauta a yanar gizo wajen tsara shiri, nazarin bayanai da alkaluma shi ma a harsuna da yawa, a ciki har da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci da Jamusanci. Dalubai kuma suna da zabin biyan $99 dan samun takardar shaidar kammala karatu.

Investigative Reporters and Editors/ masu daukan rahoto da editoci masu bincike mai zurfi suna horaswa ta yanar gizo

Google News Initiative/ Dandalin Samar da Labarai na Google –  na baiwa ‘yan jarida kayan koyon aiki, kuma sun fi mayar da hankali kan makaman aiki da google wajen samun bayanan da ake amfani da su a aikin jarida

Khan Academy/ Makarantar Khan na bayar da darussa kyauta a cikin hotunan bidiyo a yanr gizo inda suke koyarwa kai tsaye dangane da HTML, CSS, JS da SQL Languages

MIT Open Courseware tana bayar da darussa kyauta a Python, Java, da MATLAB. Kowani darasi na darasi cikin bidiyo da kuma ayyukan yi a gida.

Poynter’s News University – ta na bayar da darussa a bidiyo da kuma wadanda duk mai sha’awa zai iya yi a lokacin da yak e so. Batutuwan da ake koyarwa sun hada da nazarin bayanai, bincike mai zurfi a aikin jarida, da’a da kuma hanyoyin bayar da labarai. Yawancin darussan na bukatar biya amma akwai wadanda ba sai an biya kudi ba.

ProPublica ta wallafa darussa a YouTube dangane da batutuwan da suka shafi bayanai misali akwai gabatarwa ga code, yadda shafuka ke aiki, HTML, Basic CSS da CSS.

Workbench TrainingSuna bayar da darussa kyauta kan amfani da manhajan lissafi da yin nazarin alkaluma domin amgani da su wajen rubuta labarai ko rahotanni

The Investigative Journalism Education Consortium/ Hadin gwiwar BIncike mai Zurfi da illimi a aikin jarida na da wata hadaddiyar manhaja daga masu koyar da bayanai a aikin jarida. Shafin IJEC na kunshe da abubuwa makamantan wannan har ma da misalan irin bayanan da za’a iya amfani da su wajen koyarwa.

Our Partners
Bill and Melinda Gates Foundation
British_Council_logo
EuropeanUnion
Ford-Foundation-Logo
FPressUnlimited
gijn
HBS
Luminate
macarthur
nrgi
NED Logo
osiwa
PTLogo
ppdc

Previous
Next