Mahimman kungiyoyin da ke bayar da tallafi
- The Knight Foundation
- Ford Foundation
- Revson Foundation
- The Lenfest Institute
- Emerson Collective
- Heising-Simons Foundation
- Robert R. McCormick Foundation
- Annenberg Foundation
- Sunlight Foundation
- Shirin ‘yan jarida na Amurka
Salon samun kudi dan aikin jarida dake tashe yanzu
A duniya baki daya yanzu, kafar yada labaran da ke da ‘yancin walwala da kamanta adalci ta zama ita ce ginshikin mulkin dimokiradiyya. Sai dai, bisa rahotannin da ake samu a baya-bayan nan, kashi daya cikin hudu na jaridun Amurka sun daina aiki baki daya, sun bar miliyoyin mazauna ba tare da wata sahihiyar kafar samun labarai ba. A yanayin rashin labaran da a yanzu haka ana iya kwatanta shi da hamadar da ke cigaba da fadada.
Yanayin kasuwancin da ke dogaro kan tallace-tallacen da ya taimaka wajen dorewar jaridun Amurka na tsawon shekaru da dama yanzu ya koma ga kafofin yada labaran da ke amfani da fasahohin zamani wajen bayar da rahotanni. Attajirai da dama yanzu sun fara mamaye kasuwancin labarai. Daga cikin attajiran akwai Michael Bloomberg da Rupert Murdoch wadanda da ma sun dade a kasuwancin kafafen yada labarai kuma sun yi kudi sosai daga kasuwancin yayin da suke cigaba da al’adar sayar da labaran da ta dade a zuri’arsu (ko kadan daga ciki).
Sauran attajiran sun hada da Jeff Bezos wanda yanzu ya mallaki jaridar The Washington Post, da kuma Patrick Sonn-Shiong wanda ke da Los Angeles Times, wadanda kuma duk sun sayi kafafen yada labaran ne a matsayin wata ‘yar sana’ar da za su rika yi a gefe. Kasidar Times, ta sayi manyan kamfanonin jarida a matsayin harkokin kasuwancin da take yi a gefe. Kuma ko mun ki ko mun so Mark Zuckerberg shi ma ya zama babban attajiri ne na kafofin yada labarai. In banda kalilan daga cikinsu, yawancin manyan attajiran wadanda masu yawan bayar da tallafi ne sukan kuma yi aiki a dakunan labaransu kamar harkokin kasuwanci na gargajiya abun da ke nufin cewa su masu zuba jari ne a maimakon masu bayar da tallafi. Wannan matakin da ake dauka kan labarai ya mayar da shi abun da ya kunshi kara yawan mabiya ne kawai.
A daya hannun kuma, akwai gidauniyoyi kalilan wadanda ke tallafawa aikin jarida. Yawancin irin wadannan gidauniyoyin kan mayar da hankali ne kan abu daya takamaimai. Inside Philantrophy kab gudanar da bincike ya kuma duba irin cigaban da aka yi a fagen yadda hanyoyin samun kudin ke sauyawa da ma batun labarai na aikin jarida. Idan har kuna so ku talladawa yin fina-finan tarihi ko bayanai ku tabbatar kun duba wanna taswirar na mu film grants.
Koma bayan da ake fuskanta a wallafa jaridu da kafafen yada labarai na gargajiya da bunkasar da ake samu a soshiyal mediya wadanda ke mayar da hankali kan daukar bayanan kwastamomi a maimakon tabbatar da cewa al’umma ta sami irin labaran duniyar da ya kamata. Shi ya sa a matsayin martani aikin jarida na kyauta da kafofin yada labarai ya karu sosai a shekaru goman da suka gabata domin maido da masana’antar kan turbar da za ta iya yaki da sabbin fasahohin yada labarai na zamani.
– Hadaddiyar Kungiyar Masu Bincike a Aikin Jarida daga kasashen duniya ce ta fara wallafa wannan labarin