Sustainability / Dorewar kafofin yada labarai masu zaman kansu

Sustainability / Dorewar kafofin yada labarai masu zaman kansu

Ga mafi yawan sabbin kafafen yada labarai masu zaman kansu, kwakwarar dabara mai dorewa ta samun kudi ce kadai za ta ba su tabbacin cigaba da aikin da zai wuce shekaru biyu. Ga dai wadannsu daga cikin darussan da abokan aikin mu a kasashen duniya suka rubuta dangane da hanyoyin samun kudaden shiga, yanayin zama mamba, da gudanar da taruka, da hanyoyin samun kudi da sauran su

Sustainability: Overview/ Dorewar hanyoyin samun kudin tafiyar da kafafen yada labarai masu zaman kansu : Gabatarwa

Aikin jarida na masu zaman kansu ya cigaba da bunkasa a hanakali na tsawon shekaru 20 yanzu, bisa dalilan da aka riga aka yi bitansu, wadanda suka hada da mutuwar samfuran kasuwanci na gargajiya, da zuwan sauyi a yanayin fasahohi da ma yadda aikin jarida mai sahihanci ke samun tallafi duk da irin rikicin da ake gani a masana’antan aikin jaridar.

A wannan kundin, GIJN ta yi bincike kan irin dabarun da za su tabbatar da dorewar aikin jarida mai zurfi a kasashen duniya.

An ci sa’a yanzu ana samun karuwar wadanda ke bayar da tallafi ga aikin jarida. Wannan na samar da damammaki amma kuma yana bukatar dabaru na samun kudi dan tabbatar da dorewar kudin. Ga wadanda ke bayar da kudaden tallafi domin aikin jarida, hakan na janyo musu kalubale na musamman wadanda muka fayyace a sashen da muka kira “shawarwari ga masu bayar da tallafi.”

Bacin haka, kungiyoyin da ke aikin jarida dan samun riba, suna amfani da sabbin dabaru. Suna amfani da dabaru daban-daban wajen jan hankali da kuma hulda da masu amfani da kafar yada labaransu domin samun kudi ta hanyoyin gargajiya yadda aka saba da hade da wasu sabbin hanyoyin. Wadannan hanyoyin sun hada da biyan kudi dan sayen labaran, biyan kudi dan zama mambobin shafin, samun kudi ta hanyar karo-karo daga mutane da yawa, fadakarwa kan ayyukan kafar yada labaran, shirya taruka, amfani da kafofin sadarwa na soshiyal mediya, talla da sauransu.

Doriya a wannan fannin abu ne mai wahala ganin yadda yanayin bayanai ke sauyawa a-kai-a-kai. Wannan kundin na GIJN ya duba kalubale, damammaki, da sabbin dabaru daga fannoni da dama, kuma ya dauko ra’ayoyi da nazarin kwararru da da dama.

Shin ko akwai bayanan da ku ke so ku kara a shafin? Ku tuntube me ta adireshinmu na email wato [email protected]

Bangarorinmu sun hada da:

Sustainability: Overview/ Dorewa : Gabatarwa

Ana iya karanta bayanai mafi mahimmanci da rahotannin bincike mai zurfi da nazarin halin da fanin aikin jaridar da ba ruwanta da riba ke ciki.

Hanyoyin Tara kudi
Wannan batu ne mai mahimmancin gaske ga kungiyoyi masu zaman kansu. Kundinmu ya yi tanadin bayanai na hanyoyin gano masu bayar da tallafi da yadda ake shiga kawance da su tare da wasu karin bayanai kan hanyoyin tara kudi.

Ma’amala da masu karatu/saurare da hanyoyin samun kudaden shiga
Saduwa da masu karatu/saurare ta yin amfani da sabbin dabaru tare da taimakon soshiyal mediya zai iya habaka yawan masu sauraro da kudaden shiga. Karanta shawarwari daga editocin da ke kan kaba wajen aiki da masu saurare.

Kudin shiga na kasuwanci
Babu shakka samun kudaden shiga na da mahimmancin gaske kuma ana yin wannan wajen amfani da sabbi da tsoffin dabaru. Kwararru a nan suna binciken kalubalen da ake fuskanta wajen samun kudi daga talla, shafukan biyan kudi, biyan kudi dan sayen labaran da ma zama mamba a dandalolin labarai, da hadin gwiwa, da kawancen wallafa labarai, da‘yancin sayar da labarai da sauaransu.

Sauran hanyoyin samun kudaden shiga
Akwai sabbin dabarun da za’a iya amfani da su a madadin wadanda aka saba da amfani da su a baya, wajen tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida. Wadannan sun hada da koyarwa, horaswa, jaridu, rediyo, taruka, hadin gwiwa, kawancen wallafa labarai, biya kadan-kadan, blockchain da Cryptocurrency, sayar da bayanai, zanen shufukan yanar gizo, shirya hotunan bidiyo da sauransu.

Samun tallafi wurin jama’a
Wannan yanzu ya zama ruwan dare wajen gudanar da bincike mai zurfi a aikin jarida. Ko da shi ke, samun tallafin jama’a abu ne da ke bukatar shiri da kuma aiwatarwa yadda ya dace. Ga hanyoyin koyon wannan bisa darussan da aka samo daga wadanda suka taba amfani da shi.

Tasirin bincike
Irin alfanun da aka samu daga bincike mai zurfi a aikin jarida yana da mahimmancin gaske wajen samun goyon bayan masu bayarwa, masu karatu da sauraro da sauransu. Ba abinda za’a yi wada da sho ba ne amma kuma fada ya fi cikawa sauki. Dan haka ku ga yadda ake yi.

Our Partners
Bill and Melinda Gates Foundation
British_Council_logo
EuropeanUnion
Ford-Foundation-Logo
FPressUnlimited
gijn
HBS
Luminate
macarthur
nrgi
NED Logo
osiwa
PTLogo
ppdc

Previous
Next