Sirrin da ke tattare da samun kudi : Babbar manufa mai bukatar jajircewa
Armando Zumaya Afrilu 10, 2015
Daya daga cikin abubuwan da muka fi jin mutane na cewa a duk sadda muka bayyana mu su irin aikin da mu ke yi shi ne “Oh ni na tsani aikin tara kudi!” ko kuma “Ba zan taba yin shi a matsayin aiki ba!” Da kyau. Lallai, akwai martanoni da yawa da muka samu. Amma abun da muka fahimta shi ne ana wa samun kudi kallon wani abu mara kyau, kalubale ga da’a ko kuma dai wani abun da ba na alfahari ba ne. Mutane na ganin kamar tattaunawa da wani dangane da kudin shi tamkar tattaunawa da su kan jima’i, siyasa ko addini ne. Ba haka ba ne.
Abun takaicin shi ne ko su kansu masu zuwa neman kudin su kan yi fama da irin wannan tunanin. Su kan yi fargabar za’a yi musu kallon masu talla, a ga kamar su na da matsin lamba. Ba su so a yi musu kallon masu hadama ko kuma dai wani halin da ba shi ne ba.
Wani abun kuma shi ne babu wanda ke zuwa ya yabawa masu tara kudi kamar yadda mutanen da ke aiki a wasu fannonin kullun su ke cikin samun daukakawa da darajawa daga masu cin moriyar ayyukan da suke yi. Na mu ba kowa ya yi imani da shi ba bare ma a fahimta. Ba’a taba ganin wata lamba ta yabo wa wanda ya yi suna a ayyukan da ke kawo cigaba ba, ba za’a taba ganinmu a shafin farko na kasidu ba ko kuma ma iyaye da yaran da ke addu’a yaransu su shiga layin aikin da mu ke yi da zarar suka kai shekarun da suka dace!