Shawarwari ga Masu Daukar Nauyinmu: GIJN ta Kaddamar da Shawarwari ga Masu Daukar Nauyi

by Toby McIntosh • June 11, 2018

Yayin da ake samun koma baya a harkokin samun kudade irin na da, wannan ya sanya dole danjarida ya sauya dabarun neman kudade, haka suma masu tallafiar ayyukan ‘yanjarida ba don neman riba ba, su fadada hanyoyi da suke bi don kai agaji.

Wannan neman agaji ya zama abun bukatuwa cikin hanzari duba da yadda ake kara samun masu gallazawa da hana fadin albarkacin baki da yadda ake gallazawa ‘yanjarida. Aikin jarida ya zama wani fanni da masu tallafi ya kamata su kaiwa dauki, sai dai masu ba da tallafin na fuskantar kalubale kuma abin tambaya na zama yadda masu kai daukin za su iya auna irin tasiri na zuba jarin da suka yi.

Wadannan rahotanni na baya-bayan nan (recent reports) na Hadakar Kungiyoyin ‘Yanjarida masu Binciken Kwakwaf (GIJN) sun nutsa wajen gano tasiri na irin gudunmawa da ake ba wa aikin jarida a zamantakewa da auna nauyin tasirin shirye-shirye da ba da dabarun auna ayyukan.

 

– Hadaddiyar Kungiyar Masu Bincike a Aikin Jarida daga kasashen duniya ce ta fara wallafa wannan labarin nan