Shawarwari: Aikin jarida na sa-kai Lokacin COVID 19

Kasancewa dan jarida mai zaman kai wanda ke aikin bincike mai zurfi babban kalubale ne kusan ko da yaushe, kuma kalubalen ya karu bayan zuwan COVID-19. Kama daga kula da kai zuwa rasa aikin yi saboda matsalar tattalin arzikin da ya addabi duniya. Wahalhalun suna da yawa kuma sun danganci hali ko yanayin da mutun ke ciki.

Ga wadansu shawarwarin da watakila su taimaka.

GIJN Webinar – Wata koyarwa ta intanet ko kuma webinar mai suna Freelabce Investigative Journalism During the Time of COVID wanda aka yi ranar 9 ga watan Yulin 2020 a matsayin wani bangare na jerin rahotannin da GIJN suka yi dangane da annobar.

Bakin sun hada da Safa Al Ahmad, wani dan jarida mai zaman kan shi wanda ke fina-finan tarihi; Cecilia Anesi, daya daga cikin wadanda suka kirkiro shirin bincike mai zurfi na rahotanni a Italy; Emmanuel Freudenthal da Fisayo Soyombo, su biyun kwararru a rahotannin bincike mai zurfi; Tom Giles, babban darekta na harkokin yau da kullun a tashar ITV na Burtaniya kuma tsohon editan shirin BBC Panorama.

Hanyoyin samun kudi
  • Folio na da wani shafi na musamman wa ‘yan jarida masu zaman kansu wadanaCOVID-19 ta janyo musu wata lalura. Taimakon da su ke bayarwa ya hada da wuraren samun kudin tallafi, inda za’a sami aiki da sauran abubuwan da ‘yan jarida ke bukata
  • GIJN ta tanadar da sunayen wuraren samun tallafi wa ‘yan jarida da masu wallafa a duniya. Kudin bad an ‘yan jarida masu zaman kansu ne kadai ba amma ana iya nema
  • Gidauniyar tabbatar da walwalar ‘yan jarida ta kaddamar da wani shiri na taimaka wa ‘yan jarida da kudi. Sai dai na wani kayaddaden adadi ne na wadanda annobar ta shafa. Kudin na watan Yuli an bude shi ne a watan Yuni; ku cigaba da bin shafin dan jin sadda za’a yi wata sanarwar.
  • Kungiyar ‘yan jaridan yankin Asiya ta yi tanadin wasu kudade na musamman wa ‘yan jarida masu zaman kansu, da ‘yan jaridan da suka rasa aikin yi da sauran abubuwa masu amfani da za su taimaka mu su a lokacin annobar. Akwai wani wuri na musamman da aka tanadar wa ‘yan jarida masu zaman kansu.
  • The Overseas Press Club, ita ma kungiyar ‘yan jarida ce wadda ta tanadar da wata gidauniyar gaggawa dan samar da tallafi ga masu ‘yan jarida masu zaman kansu a watan Mayu, sa’annan ta sake kaddamar da wani a watan Yuni, dan haka ku cigaba da sa ido dan ganin sadda za mu yi wata sanarwar,
  • Hadakar kungiyoyin matan da ke aikin jarida ta kirkiro da wata taswirar da ke nuna ‘yan jaridan da ke labarai kan COVID-19. “Editoci, dakunan labaran da ke neman daukan ‘yan jarida aiki a kowani yanki na iya ganin su a kan taswirar. ‘Yan jarida na iya bin wadannan matan dan ganin ayyukansu.
Auna tasirin annobar a kan kudi

Kafofin yada labaran da suaka rage ma’aikatansu da ke zaman kansu lokacin COVID 19

Wani jerin sunayen da Study Hall ta hada na kafafen yada labaran da suka yanke kasafin kudin biyan ‘yan jaridan da ke zuwa lokaci-lokaci suna aiki da su.

Fallasa: Rikicin da ke fuskantan aikin jarida sakamakon COVID-19

Uku cikin hudu na ‘yan jarida sun fuskanci takura, kuntatawa da tsoratarwa wajen labaran COVID-19, a cewar rahoton bincike da kungiyar tarayyar ‘yan jarida na kasa da kasa ta yi kan ‘yan jarida 1,300 a kasashe 77 a watan Afrilu.

The data from the IFJ Survey.

Yaya COVID-19 Ke tasiri kan kudadend da ake biyan masu aikin Freelancing and yawan aikin da suke samu

Wani labarin da kasidar Forbes ta rubuta kan tasirin da annobar za yi kan duk wadanda ke aikin freelancing, ba lallai a fannin aikin jarida ba. Ya nuna an sami tasiri daban-daban a kan yawan akin da a kan samu da ma yawa kudin da ake biya. Kuna iya ganin wannan rahoton daga Payoneer.

Yadda Freelancers Su Ke Rayuwa da Kalubalen da COVID-19 ya Janyo Mu Su 

Wanann sakamakon wani bincike ne sa jaridar ProWriter ta rubuta inda ta gabo cewa kusan kashi 46 cikin 100 sun rasa aikinsu saboda karayar tattalin arzikin da aka samu

ProWriter found many freelancers concerned about the impact of the crisis on their income.
Kungiyoyin Sadarwa

Jaridar Press Gazette a Burtaniya ta yi rubutu dangane da bunkasar da aka samu a shafukan intanet wadanda ke daukan ‘yan jarida masu zaman kanasz lokacin COVID-19, har da adresoshin kungiyoyi da rubuce-rubucen da aka yi dangane da batun a wani labarin da John Crowley ya rubuta.

The Journalism Assembly – Wanda aka kaddamar a watan Yunin 2020 a karkashin jagorancin Cibiyar ‘Yan Jaridan Turai “domin ya kasance matattarar ‘yan jarida masu zaman kan su, inda za su hadu su yi aiki tare domin su karfafa juriyar al’ummar masu aikin jaridan freelance a Turai.” Shiga kyauta ne. “A wannan lokacin da akwai rashin tabbas masu aikin freelance suna matukar bukatar goyon baya.”

Hostwriter – wannan kungiya ce da ke taimakawa ‘yan jarida su hada kai a wurare daban-daban. Tare da kawancen Cibiyar ‘Yan Jaridan Turai ta kaddamar da COVID-19 collaboration Wire a watan Mayu, abin da ke taimakawa editoci su sami ‘yan jarida a duk duniya.

A Slack group yana baiwa ‘yan jarida tallafi lokacin rikicin COVID-19. Society for Freelance Journalists ce ta kafa kungiyar a watan Maris 2020 karkashin jagorancin Laura Oliver, wata freelancer a Burtaniya da wasu duk da hadin kan Cibiyar ‘Yan Jaridar Turai.

Following a great chat about freelance journalism work during coronavirus times with @abigailedge @mrjohncrowley @carolineharrap, here’s a way to keep talking https://t.co/Yuu04nKhQo < if you’re a freelance journalist and want to share, support+work w/other fjs right now (1/2)

— LauraOliver (@LauraOliver) March 20, 2020

Da $4 a wata studyhall.xyz na samar da damar samun bayanai dangane da editocin da ke neman ma’aikata. Ya fi mayar da hankali a kan Amirka.

Kalubalen da ma’aikatan ke fuskanta

Shawarwari 5 na jurewa rashin aiki

Shawarwari biyar din daga Journalism.co.uk sun hada da: Editoci na bukatar labarai, ku nemi kungiyoyin sadarwa, koma ga labaran baya, ku nemi hanyar kula da abubuwa da yawa a lokaci guda, ku yi iya kokarin ku ku ci moriyar halin da kuka sami kanku a ciki,

Tasirin COVID-19 a kan freelancing

Takaitacen bayani kan darasin da IJNET ta dauki nauyi dangane da freelancing. Bakin sun hada mai hada fina-finai mai zaman kanta Zoe Flood ta na magana da Melissa Noel, wata ‘yar jarida da Marc Perkins daya daga cikin manyan editocin BBC Africa Eye.

Tabbatar da Dorewar suna a matsayin Freelancer lokacin COVID-19

Wani labari daga FrayIntermedia wanda Ntombi Mkandhla ta rubuta y ace “Da yawa wadanda ke Freelancing na fama da matsala sakamakon rikicin” kuma sun yi la’akari da tasirin da aka gani a Afirca.

Jurewa tasirin Coronavirus

Wani podcast da Lily Canter da Emma Wlikinson ke tattauna hanyoyin samun kudaden shiga, raba kafa da yunkurin yin iya kokari a lokacin da ake fama da wahala.

Prevent Coronavirus from Killing Your Freelance Income

Carol Tice – Wadda ke rubutu a taskar blog mai suna-  Make a Living Writing (wato samun alfanu wajen rubutu)– ta bayar da ra’ayoyi biyar

Aiki a Matsayin Mai Freelancing Yanzu na da Wahala amma ba za’a Gaza ba

‘Yar Freelancing a Amirka Meena Thiruvengadam ta rubuta wannan wa cibiyar Pynter: A matsayin mai freelancing lokacin COVID-19, na ji kamar ina da kariya da iko fiye da yadda na zata. Amma dole ne in kai wani matsayin da zan gamsu.” Ta kuma yi wata koyarwa wa Denver Press Club.

Yadda Freelancers ke samu daga COVID-19 a yankin Asiya

A Splice Media, Meghna Rao ta rubuta rayuwar wasu ‘yan jaridan Asiya guda hudu

Jagoran Masu Freelancing kan yadda za’a kula da rashin tabbacin samun aiki a lokacin rikicin coronavirus

Wani labarin da Guilia Pines a kasidar Money Magazine ta rubuta wanda ya mayar da hankali a kan tsara yanayin amfani da kudi da yin wadansu gyare-gyare.

Da yadda ake karanci aiki yanzu, ga yadda masu freelancing za su iya yi su samu su wace wannan lokacin na coronavirus – shawarwari dangane da kudi daga marubuciya a kasidar Fortune Magazine Jennifer Mizgata.

Freelancers, wannan ne lokacin da ya kamata ku fadada kafofin samun kudadenku

Carolyn Crist tana rubutu a kai – a kai dangane da ma’aikata freelancers ta ma bayar da shawrari dangane da COVID-19

Abubuwan Karantawa wa marubuta Freelancers lokacin Coronavirus

Rebecca L. Weber wata mai freelancing a Afirka ta Kudu tana da jerin shirye-shirye dangane da irin kalubalen da ake fuskanta lokacin coronavirus a wani podcast da take yi

On the Record with Elizabeth Yuko, Ph.D.: The Press Industry in the Time of COVID-19

Hirar da aka yi da marubuciya na freelance Dr Yuko wadda ta ce ta rasa babbar kafar samun albashinta.

The Coronavirus and Freelancing: How creative professionals Are Adjusting to the Weather COVID-19

Labari kan juriya wanda Rose de Fremery ta rubuta a Skyword

To stay or go? International Freelancers Face Challenges During Pandemic

Wani labari kan sarkakiyar da masu freelancing wadanda ke aiki a wajen kasashensu na ainahi, ke fuskanta: Kos u tsaya a sabon gidan na su ko kuma su koma kasarsu ta gado Kristi Eaton, ta rubutawa IJNET

‘Yan Jarida Freelancers na sa rayuwarsu cikin Hadari lokacin annobar COVID-19.

Labarin da Dr Courtney C. Radsch darektan Kwamitin Kare ‘Yan Jarida ta rubuta

Toby McIntosh mai bayar da shawara ne a GIJN. Ya yi aiki a Bloomberg BNA a Washington na tsawon shekaru 39. Tsohon edita ne na freedominfo.org (2010-2017) inda ya rubuta manufofin FOI a duniya baki daya. Yana rubutu a taskar blog mai suna eyeonglobaltransparency.net