Membership of GIJN

Kasancewa memba a GIJN

GIJN kungiya ce mai zaman kanta da ke tallafwa masu bincike a aikin jarida a duk fadin duniya. Tun kafuwar kungiyar a shekarar 2003, GIJN ta bunkasa zuwa kasashe 80 da mambobi 203 a duniya baki daya. Mambobin sun hada da cibiyoyin rahotanni, da na koyarwa, kungiyoyin cigaban kafafen yada labarai da makarantun koyar da aikin jarida. Ga jadawalin mambobinmu a kasashen duniya, biye da ka’idojin zama mamba ma kungiyoyin da ke da sha’awar yin hakan.

Mambobin GIJN

‘Yan jarida 100, Amurka (100Reporters, USA)

100Reporters ya bi sahun kwararrun ‘yan jarida da masu fallasa da ’yan jarida masu zaman kansu a duniya baki daya, wadanda da ke aiki tukuru wajen samar da sabbin hanyoyin gudanar da aikin jarida mai sahihanci, da kuma wallafa rahotannin da suka danganci cin hanci da rashawa a duk yanayin da ya kasasnce. Kungiyar, a karkashin jagorancin fitattun wakilai na manyan kamfanonin yada labarai na da burin bunkasa irin tasiri da kuma mahimmancin bincike da labaran da ‘yan jarida masu zaman kansu ke yi a matsayin wata hanya ta inganta ayyukan gaskiya da sahihiyar gwamnati.
Shafi: http://100r.org/

Hadinkan kungiyoyin masu wallafa aiyukan bincike a Afirka (African Investigative Publishing collective (AIPC), Ghana/Netherlands)
Kungiyar AIPC kungiya ce da ta kunshi kwararrun ‘yan jarida masu bincike wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen fallasa duk illolin da ake da su a al’umma. Burinsu shi ne su gudanar da bincike mai zurfi domin gano duk wani rashin adalci ko rashin gaskiya da nufin kare al’umma, a matsayin hidima ga dimokiradiyya, gaskiya da ci-gaba.
Shafi: http://www.investigativecollective.com/

Hadakar cibiyoyin bincike na aikin jarida, Afirka Ta Kudu (African Network of Centers for investigative Reporting (ANCIR), South Africa)
A shekarar 2014 aka kafa wannan kungiyar wadda ta kunshi dakunan labarai 10 daga kasashen Afirka. Kungiyar wadda hedikwatarta ke Afirka ta Kudu na da burin karfafawa da kuma tabbatar da dorewar bincike a aikin jarida ta hanyar inganta kwarewa, tunani mai zurfi da karfin samarwa. Yayin da kungiyar ke bayar da fifiko kan “labaran da suka shafi hada-hadar kasuwanni” ta na kuma tallafawa wajen samar da horaswa da shirye-shiryen hadin kai da ababen aiki na musamman.

Website: http://investigativecenters.org/

Agencia Publica, Brazil

Agencia Publica wadda aka girkata a shekarar 20111, ta kasance kungiya mai zaman kanta ta farko kan aikin jaridan da ya shafi bincike a kasar Brazil. Wasu mata ‘yan jarida suka kafa ta da nufin mayar da aikin jaridar kasar bisa turbar da aka santa: Yi ma jama’a hidima

Website: https://apublica.org/

Hadakar ‘yan jarida masu zaman kansu, Indonesiya (Alliance of Independent Journalists, Indonesia) Wannan kungiyar da ake wa lakabi da (AIJ) tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa bincike a aikin jarida a kasar Indonesiya. Kungiyar wadda aka kafa a 1994 na da hedikwatar ta a birnin Jakarta kuma ita ce kungiya ta farko mai zaman kanta a kasar Indonesiya. Hasali ma mulkin kama karyar Soeharto ce ta yi mafari samar da kungiyar bayan da gwamnatinsa ta haramta jaridun da suka rika gudanar da bincike mai zurfi a labaransu, a ciki har da kasidar Tempo. AJI tana kuma baiwa ‘yan jarida tallafi a duk sadda a kai kararsu kotu ko kuma aka tursasa musu saboda labaran da suke rubutawa.
Website: http://aji.or.id

AmaBhungane Centre for Investigative Journalism South Africa

Cibiyar bincike mai zurfi a aikin jarida ta amaBhungane wadda a bay aka san ta da cibiyar M & G, kungiya ce mai zaman kanta wadda ke tabbatar da ci-gaban bincike mai zurfi a aikin jarida – abin da ta ke wa kallon hidimar da ta ke wa jama’a wajen habaka kafofin yada labarai masu ‘yanci, nagarta da cancanta da kuma dimokiradiyya mai kamanta gaskiya da adalci.
Website: https://amabhungane.org/

Arab Reporters for Investigative Journalism (ARIJ), Jordan

Kungiyar Larabawa ‘yan jarida masu bincike mai zurfi a aikin jarida (ARIJ) ita ce kadai kungiya mai zaman kanta a Yankin Gabas ta Tsakiya da ta dukufa wajen tabbatar da ci-gaban bincike mai zurfi a dakunan labaran larabawa, abun da har yanzu bai sami gindin zama ma. Kungiyar da ke da mazauninta a Amman, an kafa ta ne daga farkon shekarar 2005 domin ta tallafa wajen tabbatar da aikin jarida mai zaman kansa da inganci da kwarewa ta hanyar bayar da tallafin kudi ga shirye-shirye masu zurfi da kuma bayar da horaswa. Kungiyar ta na kuma taimakawa duk ‘yan jaridan da ke aiki a jarida, rediyo, talbijin shafukan sadarwa na intanet a kasashen Jordan, Syria, Lebanon, Masar, Iraki, Bahrain, Yemen da Tunisiya.
Website: http://en.arij.net/

Dandalin Aikin Jarida a Turai (Arena for Journalism in Europe)
Wanna kungiyar da ke kasar Holland na goyon bayan ayyukan hadin gwiwa, da bincike mai zurfi da aikin jarida. Ta na taimakawa ‘yan jarida da ke aiki tare a kowace kasa kuma a kowane fanni tare da malamai, da masana kimiyya ko kuma kungiyoyin fararen hula. Mahimman ayyukan kungiyar sun hada da shirya tarukan samar da bayanai wanda aka fi sani da dataharvest, babban taron ‘yan jaridan da ke bincike mai zurfi a Turai, gamayyar kungiyoyin Arena, samar da kawancen da ‘yan jarida ke bukata, da makarantar Arena – wanda ya kunshi musayar illima da hadin gwiwa a batutuwan da suka shafi bincike mai zurfi a aikin jarida.
Website: https://journalismarena.eu/

Armando.info, Venezuela
A shekarar 2010 aka kafa kungiyar Armandi.info. Wasu shahararrun ‘yan jarida guda uku a Venezuela ne suka kafa kungiyar. ‘yan jaridan sun hada da: Alfredo Meza, Joseph Poliszuk da Ewald Scharfenberg. A gajeren rayuwar wannan kungiya, Amando.info ta kirkiro shirye-shirye na musamman da abokai irin su ICIJ (Coltan/ Offshore leaks/ Swissleaks/ Panama Papers), regional newspapers as La Nación and Clarín (Argentina), El Universo (Ecuador), El Nuevo Herald y Univisión (Florida-USA), Connectas (Colombia), Confidencial (Nicaragua), La Nación (Costa Rica), Ciper (Chile).
Website: https://armando.info/

Asodiación de Periodismo Punto y Aparte
Wannan kungiyar da ke kasar Costa Rica tana tallafawa masu bincike mai zurfi a rahotanni da irin aikin jaridan da samar wa jama’a maslaha. Dandali ne na saduwan ‘yan jaridan da suka iya aikinsu, masu kuruciya kuma kwararru, yawancin kungiyoyi da mutane masu zaman kansu na samun gayyata su zo su kasance masu daukan nauyin shirye-shirye wadanda kuma ke samun goyon bayan makarantun ‘yan jarida da kafofin yada labarai. Burin kungiyar ta kunshi hada duk wadannan bangarori tare su yi aiki don samar da sabuwar shawara ga yadda za’a tafiyar da aikin jarida.
Website: http://www.puntoyaparte-ca.com/

This story was originally written by GIJN and published by the Global Investigative Journalism Network.

https://helpdesk.gijn.org/support/solutions/articles/14000036511-membership-in-gijn