Tara kudi: Batutuwan da ya kamata a yi la’akari da su
Takardar shawarwarin GFMD dangane da cigaban kafafen yada labarai, shawarwari ne da aka tsara dan taimakawa duk wanda ke neman tallafin aiwatar da shirin cigaban kafafen yada labarai ko shirye-shiryen da ke tallafawa aiki jarida.
Shawarwarin na karkashin lasisin kasa da kasa, wanda a turanci aka fi sani da creative commons attribution non-commercial share alike 4.0 international license
MARABA
Idan har kungiyarku na sha’awar samun tallafi na gudanar ayyukan cigaban kafafen yada labarai ko kuma bai tallafawa aikin jarida, kuna iya amfani da shawarwarin da ke cikin GMFD MediaDev Fundraising Guide.
Muna fata bayanan da ke ciki zai taimaka mu ku wajen samun hanyoyi daban-daban na neman tallafin, kuma zai nuna muku yadda ake tsara shiri da kyau, ya kuma taimaka muku wajen samar da tsari mai kyau — wanda zai fi samun nasara — na neman tallafi.
Wa zai amfana daga takardar bayanan hanyoyin tare kudi dan MediaDev?
Wadannan bayanan na duk wanda ke neman tallafi dan bunksada ayyukan kafofin yada labarai da tallafi dan aikin jarida.
Burin shi ne bayanan sun kasance masu inganci, kuma su taimakawa mutane da kungiyoyi wajen neman tallafinsu na farko ya kuma sake karawa wadanda suka riga suka san hanyoyin samun kudin ilimi da sabbin dabarun yadda za su inganta hanyoyin da suke amfani da su.
Ko da shi ke wadansu sassan za su fi wadansu mahimmanci bisa girma da yanayin kungiyar. Muna kokarin hada misalai na abubuwan da suka faru a zahiri dan bayar da shawarwarin da za su kwatanta yadda ya dace a yi amfani da shawarwarin tare da mahimman abubuwna da ya kamata a yi la’akari da su.
Yadda ya kamata a yi amfani da shawarwarin tara kudi dan cigaban kafofin yada labarai, MediaDev
An tsara shawarwarin ne yadda za’a rika karantawa daki-daki kowani bangare na bin na gaba da shi kuma yana dorawa a kan bayanan da aka riga aka gani.
Idan kuna so ku yi amfani da shi a haka, ba wuya, kuna iya zuwa mataki na gaba da zarar kuka latsa maballin da ke kasan shafin a hannun damar kowane shafi,
Idan har kuna sauri ne kuma kuna so ku koma shafin da kuke karantawa sadda kuka ziyarci shafin a baya, sai ku yi amfani da bayanan shafin da ke hannun hagu ku zabi kan maganar da kuke so.
Kuna kuma iya fahimtar yadda za ku yi amfani da shafin idan har kuka yi amfani da wadannan matakan
- Adiresoshin da ke cikin labarin
- Shafin da ke dauke da “Bayanan abubuwan da ke kunshe” wadanda za’a iya samu a hannun damar kowane shafi.
- Akwai kuma wurin bincike, wanda ke hannun dama a saman kowane shafi.
Idan har ba ku da layin sadarwa mai kyau, kuna iya sauke bayanin baki daya a PDF ko kuma sashin bakin daya.
Kundin koyarwa
GFMD MediaDev shawarwarin hanyoyin tara kudi na da kundin koyarwa guda goma sha daya wadanda ke mayar da hankali kan fannoni daban-daban na yadda ya dace a nemi kudaden tallafawa shirye-shiryen kafafen yada labarai da aikin jarida.
Martanoni da Sabbin sassa
Domin samun bayanai dangane da yadda abubuwa ke gudana, da sauye-sauye ko kuma samun misalai, kuna iya duba wannan sashen sa’annan ku cike fam
Karin bayani
Kalaman da ake amfani da su wajen tara kudi
A cikin kundin koyarwar duka, za ku sami adiresoshin da za su kai ku ga shafukan da ake bukata fundraising lexicon.
Kalaman na kunshe da ma’ana, karin bayani dangane da mafari, da misalai dangane da yadda ake tsara shirye-shiryen tara kudin da ire-iren kalaman da ake amfani da su wajen cigaban kafofin yada labarai , wadanda masu bayar da kudi suka fi fahimta da ma yadda ya kamata a yi amfani da su wajen neman kudin da tsarin shirin da ake nema wa tallafin.
Baya ga damar ganin kalaman bisa ka’idar jerin harrufa, ku na kuma iya ganinsu idan kuka bi irin tsarin rukunnan da aka yi amfani da su kamar haka: fundraising lexicon.
Kalaman na kunshe da ma’ana, karin bayani dangane da mafari, da misalai dangane da yadda ake tsara shirye-shiryen tara kudin da ire-iren kalaman da ake amfani da su wajen cigaban kafofin yada labarai , wadanda masu bayar da kudi suka fi fahimta da ma yadda ya kamata a yi amfani da su wajen neman kudin da tsarin shirin da ake nema wa tallafin.
Baya ga damar ganin kalaman bisa ka’idar jerin harrufa, ku na kuma iya ganinsu idan kuka bi irin tsarin rukunnan da aka yi amfani da su kamar haka:
Darussan yanar gizo-gizo
Ana iya samun shirye-shiryen GFMD wadanda ke gabatar da darussa kan hanyoyin tara kudi a na:
Idan har kuna da shawarwarin da ku ke so ku bayar dangane da abubuwan da ku ke so ku ga an tattauna, ku na iya tuntubar mu!
Hanyoyin neman kudaden gudanar da ayyukan bunkasa kafofin yada labarai.
Daga wadanne wurari ne ake iya samun tallafi?
Wannan taswirar na bayar da bayanai dangane da kungiyoyin da ke tallafawa cigaban kafafofin yada labarai da ‘yan jarida da shirye-shirye da tsare-tsare.
+ Masu tallafawa shirye-shiryen bunkasa ayyukan kafofin yada labarai
Ana iya samun bayanai dangane da masu tallafawa ayyukan tabbatar da cigaban kafafen yada labarai a wadannan rukunnan:
- Hukumomin gwamnati
- Gidauniyoyi
- Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya
- Sauran kungiyoyin kasa da kasa
- Majalisar zartarwar Kungiyar Tarayyar Turai
- Kamfanonin fasaha
- Wasu karin masu bayar da tallafi
- Kungiyoyin da ke tare kudi daga sassa daban-daban
Har yanzu muna cigaba da hada wuraren da ke bayar da tallafi. Dan haka idan har kuna so ku taimaka mana, kuna iya tuntubarmu.
Damammaki na samun tallafi
Kuna iya zuwa shafin GFMD dan ganin yadda ake samun dammamaki na kudaden tallafi a aikin jarida.
Kudin tallafi na gaggawa
A wannan shafin, za ku sami bayanai da hanyoyin samun kudaden da ake so a yi amfani da su cikin gaggawa.
+ Tallafi na lokacin rikici/ko wanda ake bukata cikin gaggawa.
Samu shiga a dama da ku
Taswirar GFMD kan hanyoyin samun tallafi dan cigaban kafafen yada labarai hadin gwiwa ce.
GFMD na samun taimakon daga mambobi 200 da kuma al’ummar da ta bayar da kai wajen ganin cigaba a yankin. Haka nan kuma muna rokonku ku yi aiki da mu wajen inganta wannan kundin na mu ta yadda zai taimakawa mutane.
Kuna iya duba sashen martanin da muka bayar kan yadda za ku iya tuntubar mu ku taimaka mana ta yadda za mu yi aiki a kan kundin ya cimma bukatun wadanda ke bukata.
Yabo
Shawarwarin GFMD dangane da hanyoyin samun kudi dan tallafawa kafafen yada labarai ya yi mafari ne sakamakon nasarorin da aka samu a wasu takardun shawarwarin wadanda suka hada da Reset’s Open Calls, da Membership Guide wanda ya fito daga shirin The Membership Puzzle Project da ma dai wasu da dama.
Hedikwatar GFMD na mika godiya ta musamman ga wadannan mutanen:
- Michael Randall, wanda ya fara kikiro da takardar shawarwarin farko.
- Kwarewa da shawarwari daga mambobinmu da wadanda ke tallafa mana bayan da suka yi bitar bayanan suka kuma kara da na su gabannin wallafa bayanan a watan Yunin 2023. Godiya ta musamman ga:
- Alex Pearce (BBC Media Action)
- Bridget Gallagher (Gallagher Group)
- Camilla Palazzini (openDemocracy)
- Laurence Burckel (CFI)
- Mariana Santos (Chicas Poderosas)
- Raquel Bennet (Chicas Poderosas)
- Shannon Meredith (Chicas Poderosas)
- Domin rubuta da kuma gyaran bayanai:
- Manuel Lemos (Intern GFMD)
- Camille Seyt (Intern GFMD)
Wa ke tallafawa taswirar shawarwaru na GFMD MediaDev?
Shirin baki daya na samun tallafi ne daga Gidauniyar Open Society Foundations.
Haka nan kuma a kan sami wani bangare na kudin daga irin kudaden da GFMD ke samu dan gudanar da ayyukanta na yau da kullun wadanda kan fito daga:
Idan har kuna so ku tallafa wajen samar da wadanda za’a kirkiro nan gaba ko kuma ma wajen fassara wannan taswirar, kuna iya tuntubar mu.
Hadaddiyar Kungiyar Masu Bincike a Aikin Jarida daga kasashen duniya ce ta fara wallafa wannan labarin