Media Liability Insurance

Ya kamata Freelancers masu aikin bincike mai zurfi su dauki inshora dan kare kan su daga zuwa kotu bisa zarge-zarge, wadanda za su iya hadawa da zagin wani, amfani da kalaman batanci, bata suna, yin kutse a rayuwar jama’a, amfani da bincike ko rubutun wani ba tare da izini ko fadin inda bayanan suka fito ba, cin zarafin hakkin mallakar rubutu da dai sauransu. Inshora za ta iya biyan kudaden daukar lauyoyi da kuma wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a biya sakamakon hukuncin kotu.

Labari mafi dadi shi ne duk freelancers da ke aiki wa kafofin yada labaran da suka riga suka kafu suna da inshoran kafar yada labaran. Idan kuma kafar ta ce za ta taimaka mu ku to ya yi. Amma duk da irin wadannan alkawuran, a kan sami akasi. Za mu yi bayani dangane da su a kasa.

Idan har kafafen yada labaran ba su yi mu ku tayi ba, samun na ku inshoran ya fi, wasu ma za su ce tilas ne.

Ana iya samun inshora mai rangwame ta hannun kadan daga cikin kafofin yada labaran da mu ka bayyana a kasa.

Duk da haka samun inshora mai kyau na da wahala, a cewar wani labarin da Laura Spiney daga Columbia Journalism Review ta rubuta a 2021

Wannan bayanin na GIJN ya duba batun ta bangare biyu: Inshoran da mutun zai samu daga kafofin yada labarai da kuma wanda zai saya da kansa.

Idan ya zo ga sayen inshora na Media Liability akwai zabi da yawa wadanda kan janyo wa mutun rudani. Amsoshin da za ku samu za su banbanta bisa la’akari da yanayin da mutun ke ciki da yawan kudin da zai iya biya.

Samun Inshora na kafofin yada labarai da bukatar shi ya banbanta daga kasa zuwa kasa. Labarin fatar baki na cewa yawancin freelancers da kafofin yada labarai haka nan su ke aiki babu inshora.

To sai dai, wata sa’a akwai kariyar da ake bukata a lokuta daban-daban. Kafofin yada labaran da ke tare da manyan kungiyoyi yawanci suna da inshora. Lauyoyin da ke baiwa masu dauko rahotanni shawara kuma na iya musu alkawarin cewa za su yi mu su aiki kyauta ko da an kai karansu kotu.

Yayin da yawancin bayanan da muke da su a kasa sun shafi yankin Arewacin Amurka ne akwai wadansu abubuwa da ke kama idan ana maganar kamfanonin inshora.

Amma watakila abin da ya fi cikin wadannan bayanan da mu ke bayarwa shi ne ‘yan jarida su fahimci abubuwan da ka iya sa su cikin matsala domin su guje su.

Kariyar Kafofin Yada Labarai

Kafofin yada labarai masu taman kansu kuma masu bincike mai zurfi su ma suna bukatar inshora ta Media Liability.

Wa ‘yan jarida da kafofin yada labarai, akwai abubuwa da yawa da ya kamata ku kula da su a duk sadda ku ka je sayen inshora ta media liability. Saboda masu sayar da inshora suna shakkan masu yin bincike mai zurfi, kafofin yada labarai na bukatar dabarun shawo kan wannan matsalar. Zabin da kafofin yada labaran ke da shi na kama da wadanda su kan su ‘yan jarida masu zaman kansu ke fiskanta a fannoni daban-daban. Dan haka muna da batutuwan da suka hadu a nan.

Kafofin Yada Labarai na Iya Sayen Inshorar

Wa masu aikin freelancing, sun ci sa’a saboda yawancin kafofin yada labarai na bas u inshora.

Akwai alamar cewa babu tsada a cewar jami’an kamfanonin isoran da GIJN ta yi hira da su.

Haka nan kuma, kare freelancers ba wai gata ne ake mu sub a. Yin hakan kan kare kafofin yada labarai daga kasha kudi da ma duk wata matsalar da aikin freelancern ka iya janyowa.

Shugabannin kafar yada labaran za su iya shawarar irin kariyar da za su bayar bisa la’akari da dangantakar su da dan jaridan. Wadansu dole a dauki shawara a lokacin da ake daukan shi aiki wadansu kuma su kan bari har sai matsalar ta taso kafin a san irin kariyar da za’a bayar. Wasu ma sukan bukaci dan jaridan ya dauki nauyin wani bangaren inshora dan saboda ko da abu ya faru ya san cewa shi ma yana da abin da zai biya.

Dan haka, idan kamar edita ya ce za’a ba ku kariya ku yi tambayoyi. Ku yi tambaya a kan lokacin da kuma nawa ne, sa’annan ko abin zai shafe ku. Idan akwai shi a rubuce, ku tambaya a ba ku kwafi ko kuma akalla bangarorin da ke dauke da abubuwan da aka shaida mu ku.

Idan edita ya ce kuna da inshora ku nemi yadda za’a aika mu ku shaida ta e-mail ko kuma a rubuta shi a cikin kwantiragi.

Watakila a yi maganan lokacin da ake yarjejeniya kuma mai yiwuwa ba zai zo da dadi ba domin wadansu kafofin za su nemi su kare kansu, amma dai ana iya tattaunawa.

Tattaunawa kan kariya

Wadansu su kan nema sun sanya duk laifin a kan freelancers amma wadansunsu sukan ki.

A kullun muna ganin yadda kafofin yada labarai su ke neman hanyoyin kare kansu yadda duk abin da ya faru ba za’a ba su laifi ba. Wannan yana da hadarin gaske. Wasu ‘yan jarida ba su karban irin wadannan kwantiragin wasu kuma su kan tattauna.

Dalilin damuwan a bayyane ya ke: Freelancers kalilan ne za su iya biyan kudin zuwa kotu bare su biya kudin hukunci idan kotu ta yanke.

A ra’ayin freelancers, wadanda suka tura su aikin su dauki nauyin hadarin.

Ga ‘yan jaridan da ke rubuta labaran da ba su da wata sarkakiya, sa hannu a irin wannan kwantiragin ba shi da wata matsala. Amma ga wadanda ke bincike mai zurfi akwai hadarin gaske. GIJN ta yi magana da ‘yan jarida da lauyoyi da kuma kwararru a fannin inshora. Ga shawarwarin da suka bayar a kasa.

Wata kila kin yarda ya yi aiki

Kai tsaye wadansu ‘yan jarida suka ki sanya hannu a irin yarjeniyoyin da ke da takuran kuma sun yi nasara.

“Yayin da yakan yi wani iri a ce wa edita ya sauya wadansu abubuwan da ke cikin kwantiragi, babu laifi idan an yi hakan idan dai ba yi shi cikin raini da tsawatawa ba,” a cewar Sara Tatelman a 2018 a shafin Story Board na Canada, wata kasidar da Kuniyar Kafafen Yada Labaran Canada ta kirkiro tare da tallafin Kungiyar Marubutan Canada domin samar da al’ummar ‘yan jarida masu zaman kansu a intanet a duk fadin Canada.

Wadansu marubutan su kan fusata da editocin da ba su da kima a idonsu su je su nemi wadansu. Daya daga cikin sui ta ce Lesley Evans Ogden wadda ta rubuta labarinta a kasidar Story Board.

Tattaunawa don rage dameji

Tattaunawa da samun kariya zai yiwu.

“Ka da ku ji tsoron tambaya a canza wadansu daga cikin sharuddan da aka gindaya (Kuma kada ku yarda a tilasta muku amincewa da abin da bai kwanta muku a rai ba),” a cewar Michelle Guillemard a wani labarin da ta wallafa a shafin Health Writer.

Bacin haka, watakila wannan na da nasaba da inshorar kafar yada labaran dan haka a yi tambaya.

GIJN ta yi hira da lauyoyi, da ‘yan jarida da kwararru a fannin inshora dangane da abubuwan da ya kamata a tattauna, ga wasu daga cikin amasoshin da suka bayar:

  • Idan sun ce har da ku a biyan inshora ku mayar da martani da abin da za ku iya biya, kada ku bari su sa muku nauyin da ba za ku iya dauka ba.
  • Kada ku bayar da kai ga batun wai daga an yi shari’a shi ke nan, ku ce abin zai shafe ku kai tsaye ne bayan an tabbatar da alhakin an kuma daukaka kara duk ba tare da yin nasara ba
  • Idan a rubutun kwantiragin an ce marubucin ya tabbatar da cewa babu wasu kalaman batanci ko zage-zage, ku bukace su da su kara kalmomi kamar “a iya sani na”
  • Ku tabbatar alhakin da za ku dauka ya tsaya a iyakacin abin da kuka rubuta, kada ka hada da abin da su suka rubuta.
Ku dauki Inshora

Idan a matsayin freelancers za ku wallafa abu da kanku, ku tabbata kun dauki inshora.

Sarkakiyar wadansu batutuwa yak e sa kafafen yada labarai su nemi taimakon kwararru.

Masana inshora yawanci sukan taimaka wajen gano inshorar da ta dace

Masana inshora kan taimaka wajen gano bukatunku. Su ne wadanda ke shiga Tsakani wajen samo farashi da kuma bayar da shawara kan wanda ya fi dacewa.

Domin samun karin bayani, Cibiyar Labaran da Ba Ruwansu da Riba wato Institute for Non-Profit News ta gudanar da wata koyarwa ta webinar da wasu kwararrun ‘yan inshora biyu daga Amurka. KU kalli wannan Video/bidiyon na 2020 da Chad Milton da Michelle Worrall Tilton.

Akwai kuma wani labari daga Columbia Journalism Review 2017 mai suna I am a Freelance Journalist. Do I Need to Buy Liability Insurance? Wanda Annalyn Kurtz ta rubuta, wadda freelancer ce mai rubuta labaran kasuwanci, kuma edit ace da ke zama a birnin New York.

Expect an Application

Domin samun inshora za’a bukaci ku cika form.

Masu bayar da inshore su na so su san kusan komai dangane da ku. Za su yi tambaya kan aikin ku, ko an taba kai ku kara kotu, abubuwan da kuke yi ku tabbatar da ingancin aikinku, kudadenku da sauransu.

Tambayoyi irin wadannan ake wa kafofin yada labarai amma sun fi haka zurfi.

Amsoshin da kuka bayar si ne za su taimaka wajen kidayar da za su yi dangane da yawan hadarin da za ku fiskanta. Wannan ne kuma zai taya su yanke shawara kan wanda za sub a ku

Akwai kuma batun kudin da masu inshoran ba su biya.

Sa’annan kuma ya na da kyau a san cewa masu inshoran ba za su taba biyan fiye da dala milliyan guda ba.

Akwai wasu karin abubuwan kuma da ya kamata a duba:

  • Wadanne matsaloli ne suke daukar nauyi? zagin wani, amfani da kalaman batanci, bata suna, yin kutse a rayuwar jama’a, amfani da bincike ko rubutun wani ba tare da izini ko fadin inda bayanan suka fito ba, cin zarafin hakkin mallakar rubutu da sauransu – Amma ya cika?
  • Duka kafafe ne ake baiwa inshoran? Har da irin su podcast?
  • Zan samu inshoran idan akai kai kara na a kasar waje?
  • Waye zai yanke shawarar ko za’a biya kudi a madadin zuwa kotu
  • Mene ne za’a iya cirewa?
  • Ana iya biyan tara ko diyyan da aka ci dan jaridan?
  • Za’a iya biya wa abin da ya faru kafin ka sami inshorar?
  • Ana iya cire kudin biyan lauyoyi?
  • Ku na iya zaban lauyoyin da za su wakilce ku?
  • Ko an kayyade kudin biyan na kowani sa’a
  • Akwai kudaden a zahiri
  • Yana bayar da kariya idan ana so a hana labarin fitowa
  • Wadansu kafafen kan kira lauyoyi su ji ko za’a iya kai ku kotu kafin su amince su sayi inshorar
  • Yaushe za’a soke inshoran