Kungiyoyin Aikin jarida na bincike
Ga kungiyi masu zaman kansu da wasu wadanda ba ruwansu da gwamnati a duniya baki daya, wadanda ke goyon bayan irin aikin jaridan da ya mayar da hankali kan bincike mai zurfi. An jera sunayen kungiyoyin daga kowane yanki. Kungiyoyi iri-iri ne wadanda suka hada da dakunan labaran da ke aiki kyauta, masu wallafa jaridu a yanar gizo, kungiyoyin kwararru, kungiyoyi masu zaman kansu, cibiyoyin koyarwa da na nazari a kusan kasashe 50. Domin tabbatar da cewa an sa kungiyoyi daga kowane bangare, GIJN ta yi amfani da wadannan sharuddan: An tsara kungiyar a matsayin wadda ba ta karban kudi, ba ruwanta da gwamnati kuma ayyukan ta na cigaban al’umma ne. Haka nan kuma, burinta ya kunshi tallafawa bincike a aikin jarida da kafofin yada labarai, tana bayar da mahimmanci ko kuma ta bayar da kai ga rahotanin shirye-shirye masu zurfi da bayanai na zahiri. Idan akwai da ku ke ganin sun dace a sanya da baku gani ba ku rubuto mana a [email protected].
Our Partners














Previous
Next