Kulla yarjejeniya

Kulla yarjejeniya ma bincike mai zurfi a aikin jarida zai yi la’akari da abubuwa da dama wadanda ba su da mahimmanci a misali labarin maguna

Akwai mahimman abubuwan da kowani irin labari ke da shi wadanda ya kamata a mayar da hankali a kai wadanda suka hada da:

 • Bayani dangane da suffan aikin da yadda za’a yi sauyi idan bukatar ta taso
 • Sharuddan biya
 • Wanda ke da hakkin mallakar labarin

Bincike mai zurfi na da wasu batutuwa da ke bukatar sa ido na musamman

 • Yadda ya kamata a biya da kyau wa babban shiri
 • Kula da hakkin mallaka
 • Yadda za’a biya abubuwan da ba’a san za’a biya misali wahen samun bayanai daga FOIA
 • Me zai faru idan shirin bai tafi yadda aka so ba?
 • Me zai faru idan wanda ya kamata ya wallafa labarin ya ki wallafawa?
 • Wadanne irin kariya na doka ne za’a baiwa marubucin?
 • Yaya za’a yi da batun inshora na hadarin da marubucin zai fuskanta?
 • Wadanne matakan kariya ne za’a bayar?
Bukatar Yarjejeniya ko kwantiragi

Watakila ba sai an jaddada cewa kuna bukatar kwantiragi ba amma lallai kuna bukata.

Idan babu, akwai yiwuwar “rashin biya, nauyin alhakin da ba naku ba, da matsaloli na shari’a,” Marubucin taskar blog a Amurka Ryan Robinson ya jaddada mahimmancin samun kwantiragi.

“Kuna bukatar kwantiragi. Ga nawa. Dauka a cewar Jyssica Schwartz a shafin Medium 2018

Sai dai ba haka yake gudana ba kullun. Yarjejeniya na iya faruwa amma dole a tabbatar cewa an san duk abin da ya kamata ya kunsa.

Me Ya Kamata Ya Kasance a Cikin Kwantiragi

Wani wuri mai kyau da ya kamata a fara shi ne Yarjejeniyar Wallafa na Model ko kuma Model Freelance Publishing Agreement a turance, wanda ACOS Alliance, wata kungiyar yada labarai ta kasa da kasa da ta kware a tabbatar da tsaro cikin harkokin da suka shafi kafafen yada labarai, tare da The Cyrus R. Vance Centre for International Justice da ke birnin New York suka kirkiro. Haka nan kuma, kuna iya duba manyan batutuwan da aka tattauna a cikin yarjejeniyar da ma samfurin ta (Duk wadannan na rubuce a cikin harshen larabci ne)

Editoci da Masu Daukan Rahotanni Masu Zaman Kansu Sun kirkiro samfurin yarjejeniya na labarai wa ‘yan jarida masu zaman kansu da kafofin da ke aiki tare da su. Kuna iya samun karin bayani daga nan/here

FIRE tana kuma taimakawa da lauyoyin kwantiragi ga wadanda ke bukata a matsayin wani bangare na shirin shawarwarin da ta kaddamar a 2021 dan tabbatar da kariya a fuskan shari’a. Kungiyar mai mazauninta a Amurka na bayar da lauyoyin da za su tattauna da wanda ke bukata na tsawon sa’a guda kamar yadda suka rubuta a shafin su a karkashin Legal Assistance. Domin samun wannan taimakon, “wanda ke bukatar wannan taimakon zai iya kasancewa a ciki ko wajen kasar – amma wajibi ne yana aikin jarida kuma ya na aiki ko shirya wani rahoton da ya kunshi labarai masu zurfin bincike wdanda ke da alaka da kafofin yada labaran da ke amfani da harshen turanci a Amurka.”

FIRE ta kuma dauki nauyin wata koyarwa ta Webinar da manyan editoci, ranar 28 ga watan Satumba 2021 dangane da abubuwan da suka shafi kwantiragi. An nadi shirin kuma kuna iya sauraro a nan/here

Ya kamata ku fahimci cewa dokoki da sharuddan kwantiragi za su banbanta bisa la’akari inda mawallafa ko kafafen yada labarai su ke.

Akwai kafofi da yawa a intanet da ke da kwantiragi. Mai yiwuwa akwai irin wanda zai fi dacewa da ku. Ku bincika kuna yin amfani da mahimman kalmomi irinsu “Model Freelance contracts” ko “freelance writer agreement” ko “freelance writing contract”

Akwai batutuwan da suka zo daidai ko’ina wadanda ya kamata a mayar da hankali kai. Wadannan sun hada da:

 • Kwatancen yanayin aikin da suke yi
 • Yadda ya kamata a kula da sauye-sauye
 • Sharuddan biya
 • Wanda ke da hakkin mallaka
Karin Karatu
 • Tattaunawa kan kwantiragi daga Canadian Media Guild
 • The Freelance Union, kungiyar da ke wakiltan dubban ma’aikata masu zaman kansu a Amurka, tana bayar da shawara kan kwantiragi
 • The National Association of Science Writers da ke da mazaunin shi a Berkeley, Carlifornia, ya na da shafi mai kyau kan freelancing, da ma bayyana kan yadda ake yarjejejniyar kwantiragi. Kuna kuma iya karanta Contract Negotiation: Getting What You Want, Gracefully, wanda Jennifer Pirtle ta rubuta a 2006.
 • The Society for Enviromental Journalists: Mai mazauninta a Washington DC wannan kungiyar ‘yan jarida masu dauko rahotanni dangane da muhalli yana karin bayani kan kwantiragi
 • Abubuwa uku da ya kamata a sani wajen yin yarjejeniya a cewar lauyoyi, a wani labarin da Maya Kroth na the Columbia Journalism Review ta rubuta a 2018
 • Freelancevoorwaarden.nl – yana dauke da bayanai har ma da manufofin freelancing kan mawallafa a kasar Holland. Kuna iya karanta wannan labarin da Linda A. Thombson ta rubuta ma Kungiyar ‘Yan Jarida na kasa da kasa a 2019
Shawarwari daga kwararru a GIJC2019

Wasu kwararru sun yi mahawara lokacin babban taron GIJC 2019 a birnin Hamburg na kasar Jamus, imda suka duba batun kwnatiragi musamman ma wadanda ke bincike mai zurfi

Babban abun dauka: Biya bisa yawan kalmomin da mutun ya rubuta a labari, duk da cewa yadda aka saba ke nan ba zai dace da labaran da bincikensu ke daukan lokaci mai tsawo ba.

A maimakon haka, masu maganan sun shawarcin yin yarjejeniyar da za ta tanadar da biya mako-mako ko wata-wata dan lokacin da aka sauka ana bincike da karin da za’a yi daga baya idan an je wallafa. A cewar bitan da Rowan Philip na GIJN ya yi dangane da mahawarar.

“Kuna iya neman wannan kuna biyanin cewa kudin kasha labarin zai kasance da mahimmanci kuma kuna iya neman sakin layin da zai ba ku hakkin mallaka. A kowani kwantiragi ku tabbatar cewa ba’a sa muku wani nauyin da bai dace ba,” a cewar Philip.

Wasu karin bayanan na da mahimmanci, misali sadda za’a biya: Lokacin da aka amince ku yi rubutun, ko daga baya, idan an wallafa.

Batun biya kafin a fara labarin idan kamar zai dauki dogon lokaci kuma zai bukaci kudi sosai? Dangane da wannan batun, freelancers sun ce ana iya tsara biyan ya kasance bayan an cimma wani buri kamar misali a ce idan an kammala hirarraki, sai a biya wani kudi kafin a cigaba.

Idan wani edita na so ya dakatar da labarin fa? Za’a biya wani kudi? Ku yi tunani sanya bayani irin wannan a cikin kwantiragin:

Idan ba’a amince da labarin bam za’a biya dan jaridan wani kudi, kashi 25 cikin 100 na kudin da dama ya kamata a biya

Duba wadannan shawarwarin kan kudaden da ake biya idan ba’a dauki rahoton ba wanda aka dauka daga labarin da Alexander Cordova ya rubuta a 2017.

 • Ka da ku sa kudi mai mai yawan gaske a matsayin wanda za’a biya idan ba’a dauki rahoton ba. Wannan zai taimake wajen kyautata dangantaka kada a rabu baram-baram
 • Ku sa farashin ya danganci yawan aikin da kuka riga ku ka yi a kan shirin.
 • Ku yi tunanin sanya wani dan tazara tsakanin sadda aka sanya hannu kan kwantiragin da lokacin da za’a fara aiki ko da wadanda suka bayar da aikin suna so su fasa.
Yarjejeniyar kudi wa manyan labarai

Scott Carney, wani dan jarida mai bincike mai zurfi wanda ya rubuta littafi mai suna “Quick and Dirty Guide to Freelance Writing,” wato jagora na rubutu a matsayin mai freelancing ya yarda cewa ana iya tattaunawa a sami kudin da ya wuce wanda ake biya wa manyan labarai.

A wata hirar da ya yi da jaridar Pacific Standard, Carney ya ce:

“wasu marubuta na wa rubutunsu kallon kayan masarufi. A ra’ayi na idan mutun ya fita ya je ya sayar da aikin shi a matsayin aikin gwaninta zai iya samun kudi mai yawan gaske. Gaskiyar ita ce idan ka fita da abin da ake so sosai za ka sami mai saye a farashin da ka ke so. Misali a wani labarin Roling Stone wanda ya sa aka kama General McChrystal. Ya kamata a ce dan jaridan ya sayar da shi wa dubban daloli amma mai yiwuwa ya sayar da shi a kan $2 wa kowace kalma.”

Wace shawara Carney ke da shi kan tattaunawa?

“Ya kamata ku yi wa aikinku kallon wani abu mai mahimmancin gaske. Na iya na tattauna kwantiragi. Na iya na samu an maido mun hakkokin mallaka na. Na iya na sami kudade masu yawa wa aiki na bayan da na ki daukan wasu ayyukan. Na kan rubuta labarai daya ko biyu ne a shekara kuma ina iya rayuwa da abin da zan samu. Saboda ina sayar da su wa farashi mai yawa ne. Ina ajiye hakkin mallaka. Ina sake sayar da labarin a kasashen waje. Ana gayyata na in yi magana. Ina kuma sayar da litattafai.”

Rike Hakkin Mallaka na da Mahimmanci.

Rike hakkin mallakar labari buri ne da kowa ke la’akari da shi, kuma gwawarmaya ne, musamman yadda ya shafi labarai na musamman.

Kwantiragin zai iya fayyaci ‘yancin da kafar yada labaran ke da shi da wanda ku za ku ajiye. Dokokin sun bambamta a kasashe daban-daban dan haka ku yi naku binciken.

Kafafen yada labarai sun sauya a cewar Jack Davies wanda ya rubuta wani labari a Columbia Journalism Review a kan “tauye hakkin mallaka” a 2018. Davies ya ce ya gano cewa kafafen yada labarai daban-daban su kan karbi duk wani ‘yancin da dan jarida ke da shi a kan labaransa.”

Su na son kwantiragi “abun da ke hana masu freelancing sama wa ayyukansu lasisi su raba da kafafe daban-daban, su sami riba kan fassara ko ma fim ko littafi, abin da ke barin su da kankanin zabi na wajen da za su sami albashin da zai biya mu su bukatun su,” a cewar Davies.

Wata hanya da za ta taimaka wajen samun ‘yancin mallaka it ace ku yi tunanin hanyoyin da ku ke so ku sami alfanu. Ga wadansu tambayoyin da za ku yi la’akari da su:

 • Ya kamata ku mallaki hakki na fina-finai, podcasts da duk wani abun da za’a yi sakamakon aikinku?
 • Za’a iya sayar da aikinku a wani harshen daban?
 • Kuna iya wallafa labarin a shafinku na kanku?
 • Wanda zai sami hakkin mallakar dindindin ne ko na wani tsawon lokaci?

Wani gargadin da kowa ya yarda da shi wato “Ku ajiye hakkin mallakarku” ya na shafin Columbia Law School ko kuma makarantar shari’a ta Columbia wanda ke bayar da takaitaccen bayani kan dokokin Amurka. Shafin na gargadin cewa:

“Idan kuka zauna baku yi komai ba, zaku kammala rayuwarku na aiki ku ga cewa kun yi abubuwa da yawa da wasu mutane ne suke mallaka ba kai, wadanda watakila ma ba wani abin da ya hada ku.”