Wallafar María Teresa Ronderos • Satimba 22, 2015
Tun daga Afurka ta Kudu zuwa Brazil; Daga Yangon zuwa Kabul na ji ‘yan jarida na magana wacce guda daya ce: Ina jin cewa ina tsaye duniya na juyawa a kasan kafata. Aikin jarida yanzu ya shiga ko’ina a fadin duniya. Nuna bukata ta jarida da mujalla ta yi kasa dubai sun ajiye.; yadda aka saba karbar tallace-tallace yanzu yayi kasa; dan abin da ake samu daga tallace-tallace a kafar intanet ba shi da yawa, yana aiki ne kawai ga wadanda suka bunkasa a kafar ta intanet.
Kafafan yada labarai sun san hanyar da za su bunkasa Facebook ko Twitter a fafutukarsu ta nemo masu neman labaransu, amma suna fuskantar kalubale na yadda za su bunkasa tasu kafar.
A fafutukarsu ta ci gaba da wanzuwa. wasu sun kaucewa hanya, ko dai su ci gaba da kasuwanci su ajiye aikin jaridar ko abu mafi muni su yi tattalin kasuwancin nasu su yi watsi da aikin na jarida.
Ina so na ba da wadannan labarai na wasu kafafan yada labarai ko ‘yanjarida daga sassa daban-daban na duniya (da dama ba abokan huldarmu bane) wadanda suka yi fafuka suka kare martabar aikin na jarida ya ci gaba da wakana duk da tarin kalubale.
Wadannan da suka yi nasara sun yi kamanceceniya ta fuska hudu:
- Sun rike kambun aikin jaridar. Ma’ana suna yin kokari su ci gaba da yin aikin da al’umma za su amfana ko da daya ne da za su iya: Su samar da bayanai, su warware abin da ya shige duhu, su gano gaskiya, abin da ke da sarkakiya su bayyanar da shi a rahoto, uwa uba yayin da aka shiga muhawara su warware lamura ta fuskar kwararru.
- Don samar da sabbin abubuwa, su kan wuce batun iyakar kafafan yada labarai. Kungiyoyi masu zaman kansu na samar da manhaja da ke ba da dama ga al’umma su san kudade da aka ware don ayyukan kwangila da aka bayar don aikin wasu hanyoyi da suka lalace wacce mutum ke daukar hotonta. Masu kare muhallai kan yi amfani na na’urar drone su dauko hotunan yadda aka lalata muhalli sanadiyar ayyukan masu fasa bututu. Duka wadannan ba aikin jarida suke ba, amma sun kasance wasu injiniyoyi da ke sadar da wasu sakonni tsakanin al’umma. Aikin jarida ya shiga ko’ina a fadin duniya. Gaba daya fannin yanzu ya samu aikin masu kutse wadanda ke samar da abubuwan da mutane ke bukata misali, Tasi ta (Uber), AirBnb(otel) da Tinder(masu hada masoya).Duk wannan na faruwa yayin da kafafan yada labarai ke tsaye suna kallon saniyar da suke tatsa na lalacewa.
- Ka yi koyi ko ka kirkiri tsarin ma’aikata da zai rika karbar sauyi. Sun gano cewa aikin jarida zai iya dorewa ba tare da dakin labarai ba, Haka nan ‘yanjarida da editoci da da masu karatu da masu kallo za su iya haduwa su tantance bayanai. Wannan alakar kuma na iya zama cikin kasa ko tsakanin kasa da kasa da za ta iya kulla kasuwanci.
- Idan suna neman kudaden shiga sai su koma hanyoyi irin na da. Sun san wa ke karanta abin da suke samarwa sai su tura talla ga wani rukunin mutane da suka tsara.(Ana kiran wannan tsari da “knowing and monetizing your metrics.”) ma’ana abin da ka sani ka mai da shi kudi, sun kuma gano tallafi a duk bangarori na abubuwan da suke samarwa a aikin yada labarai. A yau aikin masu ba da rahoton binciken kwakwaf babu tsada kamar a da duba da yadda ake samun sauye-sauye a harkar samun labarai.Suna samun kudaden shigar su ta hanyar amfani da shugabancin da suke da shi a cikin al’umma, kuma kamar gidajen jarida a karnin da ya wuce, su kan hada taruka inda za a fidda manufar kasa, a yanzu ana yi ta kafar intanet ko akasin haka, a kuma caji wadanda suka halarta da wadanda suka dauki nauyin tarukan. A karshe akwai wadanda ke sake tsari da sabunta bayanan da suke samarwa su nemi kudinsu a wajen rukunin mutane daban-daban, wadannan sun hadar da masu neman kamar masu bukatar rahoto kai tsaye yadda aka samo shi da wadanda sakonni (sms) suke bukata na musamman; bayanai na musamman/sirri, da masu neman damar tattara bayanai da dai sauransu.
Wadannan sune hanyoyi da kafafan yada labarai ke bi ta hanyar kirkira su samo hanyoyin samun kudade sabbi:
Afghanistan
Latvia
Meduza ba da dadewa ba ta kaddamar da Archanoid, wani samfurin game da ake samu a (iOS da Android), game ne da ake wasan rusa gine-gine . Abin da ake son cimmawa shine ganin gine-gine na tarihi a birnin Moscow. Ana son kawar da wasu abubuwa da suka faru a birnin a shekaru 25 da suka gabata da sunan ci gaba.
Pajhwok Afghan News na gwada dabaru 16 don ta rika samun kudade, dukkaninsu suna da alaka da ayyukanta na jarida.Daya daga cikin hanyoyi da take bi sun hadar da tattara wasu bayanai da za a iya amfani da su na fim ko rahoto da bayanan bidiyo da ta tattaro daga wani yanki don siyar wa kamfanonin dillancin labarai na kasa da na kasashen ketare, Ta kan kuma taimaka wa ‘yanjarida na kasa da kasa wadanda suka je kasarta don aika rahotanni da shirya harkokin sufurinsu da tsara taruka da yin fassara da yi wa masu bukata rakiya. Wasu kan ba da wasiku na manema labarai gare ta don ta yi amfani da hanyoyin watsa labaranta ta watsa su. sai dai ba ta neman kudi daga kungiyoyi masu zaman kansu.
Buga wannan wasa yana fito da wasu bayanai kan gine-ginen, yana ba da labarai marasa dadi kan rushe-rushe a birnin na Moscow. Wannan game ana sauke shi kyauta amma akwai wasu kyautuka da masu wasan kan siya don samun damar buga cikakken wasan.
Afurka ta Kudu
Daily Maverick kan shirya taruka The Gathering, daya daga cikin manyan taruka a fadin kasar, inda ake tattaunawa kan halin da kasa ke ciki da batun siyasa da tattalin arziki da batun adalci a tsakanin al’umma. Kimanin mutane 1,200 ke halartar wannan taro, kuma mafi akasari suna biya ne don su halarta. Har ila yau suna da masu daukar nauyi daya ko biyu daga wasu kamfanoni masu zaman kansu. A wannan shekara The Gathering, ya kasance daya daga cikin manyan abubuwa da ake ta tafka muhawara a kansu a shafin Twitter tsawon kwanaki uku kenan.
Myanmar
The Irrawaddy, da a baya ta yi gudun hijira, ta kasance mujalla da ta dawo kasar shekaru uku da suka gabata, ta samu dama cewa fannin na sadarwa na bunkasa a kasar, inda ake samun karuwar kimanin mutane 80,000 a duk wata. Sun sani cewa kashi 84 cikin dari na masu bin wannan shafin labarai nasu suna amfani ne da wayar hannu, burin da suke da shi shine su samar da manhaja kyauta amma a rika biya don samun sakonni, a hannu guda kuma su rika sanya talla da ya shafi yankinsu a bidiyonsu da suka zaba.
France
Mujallar matasa ta StreetPress ta samar da taswira da ke nuna al’adu na kusa da yanki, yankin bohemian Canal Saint-Martin a Paris. Taswirar na nuna wasu wurare masu ban sha’awa ga masu yawon bude idanu, da wasu bayanai da tarihin yankin.
Tun da a yankin ne, wannan taswira na dauke da bayanai yadda mutum ko bako zai samu wasu abubuwa na bukata cikin sauki, suna daukar tallika na kamfanoni don suna son su kai sako ga masu sha’awar kayan kamfanonin, Wannan ya nuna za su iya samo kaso daya bisa uku na kudaden da suka kashe daga wadannan hotunan da aka buga.
Wannan labari ya bayyana a watan Satumba 2015 a mujalla ta Open Society Foundation’s Program on Independent Journalism an sake gurzawa da amincewa.
María Teresa Ronderos ita ce darakta ta OSF Program on Independent Journalism, da ke fafutukar ganin an yi aikin jarida da tsari mai kyau musamman a kasashe da ke fafutukar karbar mulkin dimukuradiyya Ronderos ta zo daga OSF daga Senmana, mujalla mafi shuhura a Colombia. Ita ce ta kafa kuma ita ce editar
VerdadAbierta.com, shafin intanet da ke bibiyar yakin da ake yi a Colombia. A shekarar 2013 ita, tare da tawagarta a VerdadAbierta.com sun samu lambar yabo ta kasa Simon Bolivar National Award, wacce ake ba wa dan jarida da yayi fice a rahotannin binciken kwakwaf.
– Hadaddiyar Kungiyar Masu Bincike a Aikin Jarida daga kasashen duniya ce ta fara wallafa wannan labarin nan