Kawance da Hadin gwiwa

Hadin gwiwa a shirye-shiryen bincike mai zurfi na cigaba da samun karbuwa.

Aiki tare da abokan tarayya na iya habakawa da kuma kara yawan abubuwan da ake bukata wajen aiki da ma yawan wadanda za su karanta labaran da aka wallafa. Ana iya samun kwarewa na musamman, kamar yin nazarin bayanai, kirkiro zane-zanen hotuna ko kuma tsara shirin ta yin amfani da fannoni daban-daban na yada labarai.

Akwai rubuce-ribuce da dama dangane da hanyoyin yin hadin kai wajen bincike mai zurfi – Yadda za’a gina dangantaka mai aminci, a kirkiro dandalolin aiki, a yi musayar bayanai, a wallafa rahoton, a kula da abubuwan da suka shafi da’a da sauransu. Sai dai ba a yi rubuta da yaw aba kan yadda za’a yi “zawarcin” da ma yadda za’a tsara “zaman auren.” 

A cikin wannan jagoran GIJN ta mayar da hankali kan batutuwan da suka hada da:

  • Yaushe ne hadin gwiwa ke da alfanu
  • Yadda ake samun abokan tarayya
  • Yadda ake “zawarcin” abokai
  • Abun da ya kamata a sanya a yarjejeniya
  • Ramuka ko tarkon da ya kamata a kula

Tare da takaita darussan da aka dauka, wannan jagora za ta bayyana mu ku rubuce-rubucen da ke da mahimmanci. Yawancinsu sun yi bayani sosai, amma ba’a kan matsalolin da a kan samu da farko kadai ba, har da abubuwan da kan faru a kowani mataki na hadin gwiwar.

Yayin da burinmu na farko shi ne hadaka tsakanin kafofin yada labarai biyu, mun kuma tabo batin hadin gwiwa tsakanin kafar yada labarai da kungiyoyi masu zaman kan su wato NGOs.

Ko da shi ke shawarwari mafi bayanai da inganci dangane da hadaka shi ne wanda Rachel Glickhouse ta rubuta wa ProPublica, kafar yada labaran Amurkan da ta yi suna wajen bincike mai zurfi: Collaborative Data Journalism Guide.

Yaushe ne ya kamata a hada gwiwa?

Wasu labarin kawai sun yi girma da yawa ta yadda kafar yada labarai daya ba za ta iya yin labarin yadda ya kamata ba a cewar Bastian Obermayer, wanda shi da Frederik Obermaier suka taka rawar gani wajen fallasa labaran Panama Papers da Paradise Papers. ‘Yan jaridan na Jamus ne suka raba bayanan da su ke da shi da Hadakar kasa da kasa ta ‘Yan Jaridan da ke bincike mai zurfi wadda ke da hedikwatarta a Washington DC, wadda kuma a yanzu haka sun zama masu ruwa da tsaki a irin aikin jaridan da ke bukatar hadaka irin wadda su ka yi.

Babban abin da ke taimakawa hadaka shi ne damar da yak e bayarwa a iya gudanar da binciken da ke ketara iyakokin kasashe.

Stefanie Murray, babban darektar Cibiyar Hadin-Kan Kafefen Yada Labarai da ke jami’ar jiha ta Montclair a birnin New Jersey ta ce kwararan dalilai guda biyar ne na fara hadaka.

  • Babban taro kamar zabe na karatowa kuma yana tattare da sarkakiya dakin labarai guda ba zai iya kula da shi yadda ya kamata ba
  • Akwai rikicin da ke tasowa ko kuma ma ya faru musamman kamar labari da dumi-dumi
  • Dakin labaran ba shi da masaniyar wani bati wanda ake dauka a kusan kowani dakin labari da masu sauraro daban-daban wadanda kuma suke da banbance-banbance iri-iri.
  • Wani dakin labari na samun matsala wajen yin labari da kan shi yana ganin kamar yana bukatar taimakon wasu ‘yan jaridan.
  • Dakin labarin ya sami wasu kudaden da za su tallafa mi shi wajen aiwatar da wani shirin hadin gwiwa.

An kuma dauko wani bangaren da ta yi tsokaci a littafin jagorar ProPublica mai suna Wato shin wannan shirin ya cancanci a mi shi hadaka?

Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai ta kuma wallafa jagorori kan batutuwa guda uku da suka shafi hadin-kai:

Yadda ya dace a nemi abokan tarayya

A cewar Glickhouse “shawarar farko dangane da hadaka ga wadanda ba su taba yi ba, daga kwararru a wannan fannin shi ne za’a fi jin dadin aikin idan aka yi hadakar da wadanda aka riga aka sani.” A jagorrar ProPublica, inda aka yi magana kan yadda ake nemowa a kuma tuntubi wadanda ake neman a yi tarayyar da su, ta kara da cewa, “Kun riga kun yadda da juna kuma kuna sadawa, wadanda su ne mafi mahimmanci wajen tabbatar da hadaka mai aminci.”

“Ka da ku sa ran cewa abokan hadakar za su zo wurin ku,” bisa la’akari da shawarar farko cikin shawarwari 10 na gudanar da hadaka mai nasara tsakanin ‘yan jarida, wani labarin da abokan GIJN Guilherme Amadoo, Xing Feng, Titus Plattner da Mago Torres suka rubuta a 2018. Sun fadada batun kamar haka:

Shawara na 2 ita ce “Ku nemi abokan tarayyar da suka fi dacewa da ku”

Wanda ya fi dacewa da ku ba lallai ne ya kasance wani fitaccen dan jarida daga wata kasaitacciyar kafar watsa labarai ba. Zai iya kasancewa dan jarida mai kuruciya daga wani dan karamin dakin labarai ko kuma wanda ke aikin jarida na sa kai wanda ke da hazaka sosai. Yawancin lokuta ‘yan jarida masu kuruciya sun fi kasancewa masu dadin sha’ani saboda suna da sha’awan yin nasara, sauraon jama’a dan su fahimci ra’ayoyinsu, suna kuma da zurfin tunani. Kamar yadda ku ke yi da majiyoyi ku duba ku ga inda manufofinku su ka zo daya. Ku yi binciken mafarinsu da irin karatun da suka yi. Ku nemi wani wanda ba lallai ku na da kwarewa iri daya amma dai kuna iya tallafawa juna.

Dan haka Glickhouse na bas a shawarar gudanar da bincike kan masu dauko rahotanni da kafofin yada labaran da ke ai ki kan batun. A ganinta yana da mahmmanci a kulla kawance wajen manyan tarukan masana’antar.

Ta kuma shawarci tuntubar wadanda ke Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai dan samun shawara ko kuma duba cikin jadawalin ayyukan da suka yin a hadin-kai tsakanin ‘an jarida dan samun ra’ayoyi. Haka nan kuma ta ce ana iya yin amfani da abokai, wato ko wani ya san wani, ana iya tura sakon email ga wadanda ake sha’awar aiki da su ko da kuwa ba’a san su kai tsaye ba, da kuma tallatawa dan mutane su gani su neme ku su nuna sha’awa.

Baya ga kwarewa a fannin da ake mayar da hankali, akwai wasu bangarorin da su ma suke da mahimmanci. Wadannan sun hada da kwarewa wajen tafiyar da kungiyoyin ‘yan jarida, gudanar da shiri da kuma iya aiki da jama’a.

“Dangantaka na da mahimmanci,” a cewar Stefanie Murray a kasidar da ta rubuta wa Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai a 2018 mai suna Kuna tunanin shiga hadaka a shirin dauko rahotanni? Ga darussa 8 daga shirye-shirye 6. Ta kuma yi karin bayani kamar haka:

Shugabanin hadin gwiwa “sun yi amfani da matakai daban-daban wajen daukar ma’aikata, tattaunawa da su, kula da su da duk sauran mutanen da ke aiki da su,” a cewar wata kasidar da Joy Jenkins da Lucas Graves daga Cibiyar Nazarin Aikin Jarida na Reuters da ke Oxford (2019) su ka rubuta.

Wani abin da ya kamata a mayar da hankali a kai wajen zaben abokan tarayya ya taso a babban taron GIJN da aka yi a birnin Hamburg a 2019. Wata sa’a a kan zabi abokan aikin “tun kafin a kammala bincike yayin da aka sami bukatar fara wasu rahotanni.” Wannan sakon ya zi daga wurin Axel Gordh Humlesjö, wani mai daukan rahotanni da ke aiki da gidan talbijin na Sweden wato SVT kamar yadda aka kwatanta a cikin kasidar da Rowan Philip ya rubutawa GIJN. Humlesjö ya kara da cewa:

Wani jagoran daga Ofishin kula da Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida a Burtaniya wato Bureau of Investigative Journalism wanda ya fara baiwa al’umma karfin gwiwar shiga a dama da su, na tuna mana cewa ana iya yin kawance da wadanda ba ‘yan jarida ba:

Nan gaba

Zaben abokan tarayya shi ne matakin farko.

Shawarwari kan matakan farko da ya kamata a dauka yayin da ake kokarin fara hadakar na da mahimmanci ga yanayin zaben. Abun da ake ta maimaitawa shi ne ku tabbatar akwai yarda a tsakaninku. Ga wasu rubuce-rubuce da za su iya taimakawa:

  • Bitan samar da kawance da yarjeniyoyi, MOU da sauran abubuwan da akan yi a hukumance sassa a jagoran ProPublica
  • Karanta shawarwari na 3-10 daga kasidar da aka yi bayani daga farko kan shawarwari 10 na gudanar da hadaka mai nasara tsakanin ‘yan jarida
  • Karanta kasidar Stefanie Murray Kuna tunanin shiga hadaka a shirin dauko rahotanni? Ga darussa 8 daga shirye-shirye 6.

Wasu rubuce-rubucen da za’a iya dubawa kuma wadanda ke dauke da darussa daga ayyukan da aka yi a baya da misalai da hadin gwiwa da sauransu:

  • Global Teamwork: The Rise of Collaboration in Investigative Journalism, “littafin da aka wallafa a 2018 wanda Richard Sambrook ne edita kuma Cibiyar Nazarin Aikin Jarida ta Reuters ce ta dauki nauyin wallafawa.  A babi na 5 darektan shirin Anne Koch ta yi bayani kan yadda ‘yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu za su iya – kuma ya kamata su yi aiki tare.
  • Cross-Border Collaborative Journalism: A step by Step Guide,” Littafin da Brigitte Alfter ta rubuta a 2019
  • Cibiyar Hadin-Kan Kafofin Yada Labarai wanda ke makarantar sadarwa da kafafen yada llabarai na Jami’ar jiha ta Montclair na da bayanai da dama a shafukanta, a ciki har da: shawarwari da fitattun ayyuka da kundin ayyukan da suka gudanar.
  • Collaborative Journalism Workbook wanda Project Facet suka shirya.
  • Collaboration dand the creation of a New Journalism Commons rahoto mai zurfi wanda Carlos Martinez de la Serna, dalubi a Cibiyar Tow na Aikin Jarida na Dijital da kuma dan jarida da bincike da ke zaune a birnin New York.
  • Collaboration on the Pegasus Project added risks for corruption reporters/ Hadakar da aka yi a shirin Pegassus ya kara hadari ga masu dauko rahotannin cin hanci da rashawa.