Kariya a fannin shari’a

Kariya a fannin shari’a

Duk fadin duniya, dokokin da suka shafi ‘yancin ‘yan jarida na fadan albarkacin baki da samun bayanai, kullun cikin sauyawa suke – kuma samun rauni a jiki ko a fanin kudi su ne mafi yawa a cikin matsalolin da ‘yan jaridar su ka saba fuskanta. Dan haka sanin cewa akwai kungiyoyin da suka amince su kare wadannan dokokin wadanda yankuna, da kasashe, da al’ummar kasa da kasa suka girka ba karamin ni’ima zai bai wa ‘yan jarida ba. To sai dai kungiyoyin agajin shari’ar su na da iyaka, domin wata sa’a aikin su zai halatta ne a yanki guda ko kuma wani fanni na shari’a. Ga dai wasu daga cikin kungiyoyin da su ka riga suka kafu, wadanda kuma sun kware wajen bai wa ‘yan jarida shawara, tare da wadansu shawarwarin da ka iya taimakawa:

Kungiyoyi

Shirin Kare Dokoin Kafafen Yada Labarai MLDI (Na kasa da kasa)
Wannan kungiyar ta kasa da kasa wadda ba ruwanta da gwamnati tana taimakwa wajen kare ‘yancin ‘yan jarida a kowace nahiya kuma a kowace kafa ta yada labarai – kama daga jaridu zuwa talbijin da rediyo har zuwa yanar gizo-gizo. Kungiyar wacce mazauninta ke Landan na aiki da wasu kungiyon kare dokokin ‘yan jaridar da ke kasashen duniya da ma lauyoyi masu zaman kansu. Sa’annan idan ya kama za su biya duk wani kudin da ake bukata wajen shari’ar. MLDI ta fi ba da fifiko ga ‘yan jarida masu zaman kansu, wadanda ke fuskantar barazanar zaman kurkuku ko rashin dukiya da ma durkushewar kafar yada labaran. Haka nan kuma ‘yan jarida suna samun taimako a duk sadda suke bukatar jaddada ‘yancin su. A shekarar 2019 MLDI ta kaddamar da shirin kariya ta shari’a mai tallafawa masu binciken gaskiya.

Asusun kare ‘yancin ‘yan jarida kyauta – tallafin kudi wa ‘yan jarida da kafofin yada labarai a duk fadin duniya. “Mu na bai wa ‘yan jaridan da ke fuskantar tuhuma ko hukuncin dauri, wadanda ba su da halin daukar lauya ko kuma biyan kudaden da ake bukata.” Domin karin bayani ana iya tuntubarmu ta e-mail da adireshin [email protected] ko kuma ta ya waya a ofishinmu Free Press Unlimited Office da lambar: +31208000400

Ofishin Wakili na Musamman kan ‘Yancin Fadan Albarkacin baki (na kasashen yankin kudancin Amirka)

Wakilin na musamman na aiki ne a matsayin mai bincike. Aikin shi ya tanadi gudanar da bincike kan rubutattun kararraki da korafe-korafen da ‘yan jarida suka turo, sa’annan sai ya rubuta rahoto ya tura wa Hukumar hadakar kasashen nahiyar Afirka kan hakkin dan adam (IACHR) dangane da take hakkokin ‘yan jarida. Daya daga cikin mahimman ayyukan wakilin shi ne bai wa IACHR shawara kan kararrakin da aka rubuto ya kuma shirya rahoto dangane da su. Bisa wadannan shawarwari ne IACHR za ta shigar da kararrakin da korafe-korafe a gaban kotun hadin kan kasashen Amirka kan hakkin dan adam. Duk da cewa wakilin ba ya baiwa ‘yan jarida da kafofin yada labarai shawara ko tallafin kudi, a kyauta ya ke tantance kararrakin da ‘yan jaridar suka rubuta.

Pers Vrij Heids Fonds (Netherlands)

Kungiyar ‘yan jarida masu amfani da harshen Dutch tare da hadin kan al’ummar editocin Netherlands suka girka Gidauniyar Asusun ‘yancin ‘yan jarida a shekara ta 2007 domin su tallafa wajen kare hakkin ‘yan jarida na fadan albarkacin baki da ‘yancin samun bayanai. Duk da cewa matsugunin Asusun na Amsterdam ne kuma ya fi bayar da fifiko ga al’ummar kafofin yada labaran Dutch, Asusun ya tallafawa ‘yan jarida da dama a wasu kasashen Turai.

Kwamitin manema labarai kan ‘yancin walwalar ‘yan jarida (Amurka)

Baya ga layin waya na gaggawar da ta samar musamman saboda ‘yan jarida (Har da dalibai) da ma’aikata a fanin shari’a, wannan kungiyar mai zaman kanta da ke da shelkwatarta a birnin Washington D.C. na bayar da shawarwari kan wuraren samun taimako da kuma bayani kan hukunce-hukuncen kotu da ma sauran labaran da ke da dangantaka da dokokin yada labarai. RCFP ta kan buga littafin dokar da ta shafi ‘yancin fadar albarkacin bakin ‘yan jarida a Amirka wanda aka fi sani da First Amendment a turance. Littafin ya fayyace mahimman batutuwan da suka shafi ‘yancin d ‘yan jarida na tara bayanai da yada labarai da kuma Rigar Kariya ko Gatar ‘Yan jarida, cikakken bayani dangane da ire-iren kariyar da dan jarida ke shi – misali ba za’a iya tilasta wad an jarida ya bayyana majiyoyin bayanan shi a kotu ba – a kotunan jihohi da na tarayya. Domin samun bayanan jama’a daga gwamnatin tarayya ko ta jiha ko ta karamar hukuma, ana iya amfani da manhajar Kwamitin Masu Dauka labarai mai suna iFOIA wanda ake samu a yanar gizo. Akwai kuma shafin FOIA Wiki wanda ke kwatanta dokar ‘yancin samun bayanai na FOIA da hukunce-hukuncen kotu dangane da kararrakin da suka shafi ‘yancin samun bayanai.

The open government guide/ Budaddiyar taswirar gwamnati ta kwatanta duk bayanan da jihohi suke da shi a bude, da ma dokokin tarukan da ake yi a bayyane. Akwai kuma shurun sanya ido kan sadarwa: abin da ya dace ‘yan jarida da gidajen yada labarai su sani.

Asusun kare doka/shari’a ta al’ummar kwararrun ‘yan jarida (Amurka)

Makasudin samar da wannan asusun shari’ar shi ne “kadamarwa da kuma tallafawa shari’ar da za ta tilasta gwamnati ta bai wa jama’a damar samun bayananta da aikace-aikacen da ta ke gudanarwa” amma kuma ana iya amfani da shi wajen shiryawa, sanarwa da ma jan hankalin jama’a domin a taru a tabbatar da samun bayanan gwamnati da ayyukanta. Duk da cewa babban burin asusun shi ne samar da kudaden da za’a taimakawa ‘yan jarida, ofishin na iya taimakwa wajen zaban lauyan da ya lakanci dokokin fadan albarkacin baki na “First Amendment” a duka jihohi 50 na kasar.

Karin Bayanai

Littafin tsaro na ‘yan jarida da masu rubutu a taskokin blog – Kungiyoyi da dama suka ada wannan littafin mai shafuka kusan 300. Daga cikinsu akwai Reporters Without Borders ko kuma ‘yan jarida marasa iyaka, gidauniyar Thomas Reuters da wani kamfanin lauyoyi na kasa da kasa mai suna Paul Hastings LLP. Sassan littafin sun hada da Martaba da batanci, Dama na sirri, tsari na jama’a da halin kirki, tsaron kasa da sirrin kasa.

Shawara: Kare kai daga barazanar doka, daga Kyu Ho Youm.

Shawarwarin UNESCO ga masu shigar da kara: Wannan rahoton ya bayyana shawarwari daki-daki wa masu shigar da kara na yadda za su tafiyar da shari’o’in miyagun laifukan da aka yi wa ‘yan jarida a harsuna takwas, wadanda suka hada da: Turanci, Portuganci, Rashanci, Larabci, harshen Indonesiya da na China.

English Version

Our Partners
Bill and Melinda Gates Foundation
British_Council_logo
EuropeanUnion
Ford-Foundation-Logo
FPressUnlimited
gijn
HBS
Luminate
macarthur
nrgi
NED Logo
osiwa
PTLogo
ppdc

Previous
Next