Samun inshora yayin da ake gudanar da bincike a labari mai tattare da hadari na da amfani kuma watakila ba shi da irin tsadar da ku ke tunani. Kafar yada labaran ta na iya biya.
Me za’a biya wa inshorar?
- Matsalar tafiya: Ko da an Makara wajen zuwa kama jirgi, takardun tafiya sun bata da sauransu
- Kiwon Lafiya: Kamuwa da cuta ko Jin ciwo (Banda abubuwan da ke da dangantaka da COVID-19
- Fita wato evacuation daga wata kasa ko wani yanki idan ta kama dole
- Ko da an yi garkuwa da mutun
- Inshora na wata nakasa
- Dawo da gawan mutun idan ya rasa rai a bakin aiki
- Ko da kayayyakin aiki sun bata ko sun lalace.
Gidauniyar Rory Peck, wata kungiyar da ke Burtaniya wadda ke tabbatar da kariyar ‘yan jarida masu zaman kansu na da bayanai dangane da ire-iren inshoran da za’a iya samu da ma irin abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su idan har za’a nemi kamfanonin inshoran.
Wadannan bayanai suna nuna irin tambayoyin da ya kamata a yi da kuma matsalolin da ya kamata a kaucewa.
Samun kafar yada labarai ta rubuta inshorar aiki mai hadari a cikin kontiragi abu ne mai matukar alfanu. Akwai zabi uku na yin haka, kamar yadda aka rubuta cikin samfurin kwantiragin da ACOS Alliance – Kafin da ta goge wajen kula da harkokin tsaron da suka shafi kafafen yada labarai – ta rubuta.
ACOS tana bayar da shawarar:
- A nemi kamfanin da sanya freelancer din a cikin shirin ta na tafiye-tafiye.
- Dan jaridar na iya fansar kudin da ya biya dan inshorar da ya dauka a dalilin aikin
- Ana kuma iya sa freelancer din ya tambayo nawa ne kudin inshorar da ya ke bukata tun farko, sai a sanya shi cikin kudin da dama za’a biya saboda aikin
Zabi Daga Kungiyoyi Uku
Akwai kamfanoni da yawa a duniya da ke sayar da inshora na tafiya, amma kamfanonin masu yada labarai sun kan hada kai da kamfanonin inshora masu zaman kansu wadanda ke da shirye-shirye na musamman dan masu aikin freelancing.
ACOS Alliances tana taimakwa bayar da damar samun inshoran tafiya da kuma wanda kamfanonin ke saya wa freelancers yayin da su ke aiki a kasashen waje. Dukkansu ana bayarwa ta hanyar kamfanin inshoran Burtaniya InsuranceforJournalists.com da ragen kashi 7.5 wa kamfanonin da ke amfani da shika-shikan su, na tabbatar da kariyar Freelancers (Freelance Journalist Safety Principles) An kaddamar da ACOS a shekarar 2015 a matsayin kungiyar hadin – kai tsakanin kungiyoyin yada labarai, kungiyoyin ‘yan jarida freelancers da kuma kungiyoyin tabbatar da walwalar ‘yan jarida.
Takardun tafiyar na bude wa duk ‘yan jaridan da za su yi tafiya zuwa kowace kasa da duniya, har da kasashen da ake yaki. Ana sabunta inshorar kowani mako kuma abubuwan da ya tanadar sun hada da mutuwa da jin irin ciwon da ya janyo nakasa, ciwo da kuma magunguna idan an yi hatsari na akalla $250 da kuma zuwa asibiti cikin gaggawa. A duba wannan shafin da karin bayani.
Akwai kuma wani shirin mai rangwame wanda ake baiwa wadanda suka san gari suna taimakawa wajen hada dan jarida da wadanda yak e bukata, wadana ke aikin producer a yankin da aka kai ziyara, masu fassara, da duk sauaran ma’aikatan kafafen yada labaran da ke taimakawa da aikin. Ana iya daukar inshoran wa duk wadannan mutanen a ko’ina suke aiki a duniya, wato ciki da wajen inda suke zama.
Masu Dauko Rahotanni Ba (RSF) na bayar da inshora na lafiya da kuma maido ‘yan jarida gida wadanda suka je aiki a kasar da ba ta su ba, har da yankunan da ke fama da yaki, ko da shi ke akwai wadansu wuraren da ba’a zuwa. Kasancewa memba a RSF tilas ne.
Tare da hadin gwiwar kamfanin inshoran Escapade RSF na bayar da wani shiri da ake kira “Essential Plan” wanda ke nufin shirin da ake bukata. A karkashin wannan shirin ‘yan jarida za su sami inshora a ko’ina a duniya ban da kasashen su na ainihi da kuma wuraren da ake musu kallon suna da hadarin gaske, kasashe irinsu Afghanistan, Crimea, Iraki, Somalia, Sudan, Kudancin Sudan, Syria, Zirin Gaza da Yemen. Sai dai kuma akwai wani shirin na musamman da ake tanadarwa wadanda za su je wadannan kasashen wanda ake kira “Extended Plan” “amma masu dauko rahotannin da ke zama a Amurka da ‘yan Brazil da ke zama a Brazil da ‘yan Canadan da ke zama a Canada ba su cancanta ba.”
The International Federation of Journalists na da kawance da wani kamfanin inshoran Burtaniya mai suna Battleface wadanda su ke baiwa mambobinsu inshora na tafiya da magunguna da kuma na fita idan ya kama. Akwai kuma zabin karbar inshorar wa kayayyakin aiki. Ana iya duba shafin Battlface don samun karin bayani.
Farashi
Tunda farashi kan kasance babban matsala bari mu duba shi.
Mun duba wurare uku ta tare da la’akari da abin da suka fi mayar da hankali a kai dangane da manufofi ko shirye-shirye ba.
Na tsawon mako guda a kasar da ke da hadarin gaske farashin na tsakanin $80 da $105. Farashin bai kai haka ba a wuraren da babu barazanar rashin tsaro. Mako guda a kasashen da ke zaman lafiya na tsaknain $18 da $32.
Farashi daga shafin insuranceforjournalists.com na cikin wani jaddawali da aka kirkiro a 2016 inda aka auna hadarin kasashe aka sanya su cikin rukunnai biyar daga mafi hadari zuwa mara hadari. A kasar da ke cikin mafi hadari irinsu Libiya inshora na mako gida $80 a yayin da a can mara hadari kuma $24
Reporters without Borders ta na bayar da $18.48 a mako a shirin ta mai mafi karancin farashi, babu bayanin abin da ta ke biya a kasashen da ke da mummunar hadari. Wani jami’I da ke aiki da kamfanin inshoran su ya ce idan aka yi misali da wuri kamar Siriya “kimanin $55.82 a rana na tsawon mako guda wanda ke zaman akalla $390 a mako.
Kamfanin Battleface za ta baiwa ma’aikacin kafar yada labaran da ya je Siriya $105 a mako. Farashin zai zama $32 a wuraren da babu yaki.
Ku tuna cewa ba lallai ne wannan ya kasance daidai ba, dan sanin gaskiya ku yi bincike da kanku a shafukan wadannan kamfanoni ko ku tuntube su kai tsaye.
Wasu karin Zabin
Kamar yadda aka bayyana a sama, yawancin kamfanoni na bayar da inshora na tafiya, kadan ne ke da shirye-shiryen da aka tsara takamaimai don ‘yan jarida. Akwai gajeren jerin sunayen kamfanonin da ke tausayawa ‘yan jarida Freelancers da gidauniyar Rory Peck ta yi tanadi a shafinta.
Kuna kuma iya duba shafukan:
- Yonder
- Bellwood Prestbury