Hanyoyi tara na inganta yadda ake rubuta takardun neman tallafin aikin jarida

Wallafar ERIC KARSTENS

Oktoba 30, 2018 a MEDIA SUSTAINABILITY

Tallafi na ‘yanjarida ba shi da yawa sai dai komai kankantar sa zai iya kawo maka sauyi a aikinka. Idan za ka iya samun kimanin EURO 1,500 na iya taimaka maka ka je wasu wurare da kake dauko rahoto ko ba komai wadanda ke karanta aikinka sun san cewa kaine da kanka ka je wajen ka dauko rahoton.

Wasu ayyuka da ke zama na musamman na iya jawo samun kudade masu yawa kamar na Innovation in Development Reporting  (Gargadi: Ina ba da tawa gudunmawa wajen aiwatar da wannan ayyuka ta bayan gida) Manyan kudaden tallafi kan iya daukar nauyin baki dayan ‘yanjarida da masu daukar hoto da kwararru da masu tsara zayyana da kwararrun tattara bayanai da masu tsara code a kwamfuta da dai sauransu. Yayin da suka dukufa wajen gudanar da wani aikin binciken kwakwaf wanda ba kowace kafar yada labarai ba ce a yanzu za ta ma iya sa kanta aiwatar da wannan aiki.

A kankin kaina na shiga huldodi na hada-hadar neman kudaden tallafi ta fuskoki da dama ga misali daga mai rubuta takardar neman tallafi, ko kwararren mai ba da shawara a aikin neman tallafi, a wani lokacin ma na kan shiga aikin tantance wadanda suka cancanci samun na tallafi a matsayin alkalin tantancewa. A wannan mataki na gano wasu kura-kurai tara da masu neman tallafi kan yi, musamman masu neman tallafi daga bangaren ‘yanjarida. Wannan shine abin da na lura saboda ‘yanjarida ba kamar masu aikin kungiyoyi ba, wadanda kan dauki labarinsu zuwa ga edita da zai ce a cire wannan a bar wannan, kawai su je su ci gaba da aikinsu, tsara takardar neman tallafi ba kawai batu ne na fidda tsari mai kyau ba, akwai tari na sarkakiya a tafiyar, ta yadda tallafin kan zama na mai rabo.

Wadannan sune jerin kura-kuran da kan kassara ayyukan ‘yanjarida kafin ma su kai wani mataki, Domin fayyace bayanai ana iya ganin kamar ina kambamawa amma ba haka ba ne.

1. Ba a karantawa a fahimci sharuda da ka’idoji

Abin mamaki ne yadda wasu masu rubuta takardun neman tallafin ke nuna karancin ilimi na aikin da suke nema. Alkalai suna gano irin wannan suke watsi da su, ko da kuwa a kan kansu suna da wata martaba. Domin ta yaya ne aikin da aka ce misali zai nazari kan ci gaba na baya-bayan nan kan kimiyar halittu masu rai zai bige da daukar nauyin rikicin ‘yangudun hijira? Don haka ina ba da shawarar a karanta sharuda da ka’idoji ba sau daya ko biyu ba. A karanta yadda ya kamata. Za ka sha mamakin abin da za ka gano bayan dogon nazari na sharudan da ka’dojin. Domin suna da alaka…

2. Sauka daga kan manufa

Koda a ce sun dauka hanya tiryan-tiryan a rubuta takardun neman tallafin, sannu a hankali sai su sauka daga kan manufar ba da tallafin. Idan ana da bukata daga kasashe da ke koma baya least developed countries kada a zo da bukata daga wani waje da ke zama kauye a kasar Jamus, wani na iya ganin ta yaya haka za ta faru, ni kuwa na ga tarin misalai. Ka mayar da hankali kan manyan ajandodi, ka yi abin da ka koya a matsayinka na danjarida wato gudanar da bincike don fahimtar abin da me ba da tallafi ke bukata. Kuma ko da ka yi hakan akwai kuma…

3. Rashin bayyana abu kararan

Wasu takardun neman tallafin da a kan kawo, su kan cika sharudan da manufar shirin sai dai sukan gaza kuma wajen bayyana takamaimai irin labarin da za su bayar. Bukatar neman gudanar da bincike kan harkokin cin hanci da rashawa na da kyau, masu binciken na son ganin ka ba da misali na wani aiki da ka yi sananne, ba kawai bincike ba, a ce an samu wani aiki da ka yi da ya zama sananne. Ka tabbatar da yin binciken ka kafin fara rubuta takardar neman tallafi- Ka gudanar da binciken farko, ka tabbatar da abin da ka zo da su gaskiya ne, ka duba ko kana bukatar wasu abubuwan kafin ka gamsar da wanda za ka yi wa aiki, Saboda akwai kuma bukatar…
4. Rashin yin cikakken bayani a kanka

Labarai da dama an gwada basira wajen ba da su kuma sun cika sharudan ba da tallafin. Sai dai a wajen takardun neman tallafin suna gaza bayyana hakan.Abin da ke zama abin mamaki ga ‘yanjarida ganin cewa wannan shine abin da ya kamata ya zama aikinsu. Amma sai a samu an dunkule komai wuri guda, don ana yin sauri ko a ba da bayanan da ba su cika ba, ko ba a damu da ba da bayanan baki daya ba.
Mu dauka alkalin da zai nazarci bukatun bai san komai ba kan aikin da kake son yi ko da dai shi ma na da nasa ilimin, idan ka dauka kana magana da wanda bai san komai ba a fannin, za ka fi kokari wajen fito da bayanai. Matakin da zai sa aikin ka ya fi karbuwa. Amma akwai wani aikin gaba:
5. Gaza gamsar da mai ba ka tallafi cewa za ka iya aikin.

Wasu takardun neman amimncewar suna da duk abubuwan da ake bukata da aka bayyana a sama, amma sai su gaza nasara saboda gazawa wajen nuna kwarewa kan yadda za a yi aikin. Wani lokacin kuma sakaci ne ko gidadancin cewa ba ka taba zuwa Afurka ba, Mai amincewa da bukata ko alkalin da ya duba takardunka babu shakka ba zai bari ka yi tafiya zuwa Kwango ba, saboda suma sun damu da walwalarka kuma ba za su so su yi asarar kudadensu na tallafi ba. Ana iya binciken kwarewa ta fuskoki da dama, idan ka dade kana aikin ba da rahoto ka ba da CV da wadanda za a iya tuntuba cikin sauki, idan kuma ba ka taba irin wannan aiki ba ka bayyana cewa ka yi bincike a kansa kuma kana da wasu dabaru da kake son amfani da su don tunkarar aikin.

6. Ka nuna cewa kai ya kamata ka samu wannan tallafi

Wasu takardun neman tallafin kan samu kai yanayi na kame-kame kan cancanta ko da suna da basirar ba da labarin, wannan na faruwa idan babu kamanceceniya tsakanin mai rubutawa ko masu rubutawa da aikin da za ayi. Ga misali fitacciyar mai ba da rahoto kan wasanni ta ce za ta gudanar da bincike kan karuwar makaman nukiliya. Wannan na iya bayiwa cewa alkali ya ce ta zo ne neman aikin don neman kudi ba don tana da sha’awar aikin ba. Yana da kyau aikin da za ka nemi tallafi a kansa shi ne kake yi har kawo yanzu, idan kuma sha’awar kake yi sai ka yi gamsasshen bayani. Idan ba haka ba kuwa alkalin da ke duba takardun neman tallafin na iya tunanin…

7. Jin cewa kai wani ne

Wannan na faruwa ga wadanda suka yi shuhura a aikin jarida, sun rigaya an sansu a wani bangare ko suna aiki da wata kafar yada labarai da kowa ya santa yake mutuntawa-mafi muni, Idan suna aiki a gidan talanbijin da zarar sun je neman abu kowa ya sansu idan sun zo suna magana da ‘yansiyasa su tattauna kan ko menene. Me zai hana alkalan su ba su tallafin idan sun je nema? Tabbas hakan na iya taimakawa idan ka yi suna kan tsayawa kan munafa da bayyana ra’ayi, duk da haka alkalan kan kuma duba batu na dattako, Ka tsaya a tsanake ka rubuta bukatarka kamar kowa ta gamsar ta ja hankali ka kaucewa… 

8. Kada ka tura kasafi kunshe da rashin gaskiya ko mara dalili

Kasafi abune da ake son ya karbu, ayyukan ‘yanjarida ba za a bar su a baya ba, Babu tantama abu ne kuma mai wahala a yi hasashe na kudade da duk abubuwan da ke bukata na kudi da za su zo a gaba. Kura-kurai a iya afuwa. Akwai kasafin da ake samu, wadanda suka nemi tallafi na aringizo na kudaden albashi kan aikin da suke yi, ko suna da burin ajiye wasu kudade ta hanyar kara kudaden wasu kayayyaki. Sai dai alkalan na da masaniya kan abin da ‘yanjarida ke samu da mai za su iya kashewa zuwa wasu gurare na musamman da tsawon wani lokaci za su dauka don ba da rahoto a kan kari. Kada ka ce za ka kashe kudaden masu ba da tallafi idan ka yi aniyar lp sha’awar zuwa bakin ruwa a karshen mako.

9. Canki-canka kan bukatun bayani daga masu ba da tallafi

Abu na karshe wanda shi ake kammalawa da shi. Masu ba da tallafi da dama suna da wasu hanyoyi na musamman da suke aiki dama yin tunani. Suna iya bin irin na logical framework approach, wadanda kan so a bude ayyukan da ka karshe, ko a tambaye ka ka cike fom ko a nemi ka cike fom da zai cimma bukatun ofisoshin haraji ko hukumomi masu sa idanu don amsa tambayoyi. Wannan kan kawo rudani da rikitarwa musamman ga wadanda ke neman tallafin a karon farko. Hanya mafi sauki ta cimma wannan ita ce tambayar wadanda suka amfana da irin wannan tallafi a baya. Ko ba komai sun yi, an ga nasarar da suka cimma. Ana iya nazartar irin wadannan, ka duba a tsanaki. Kada ka samu sagewar gwiwa, akwai tari na tallafi masu kyau da ake warewa ‘yanjarida — Suna da yawa fiye da ayyukan ma da ake yi yanzu , abu da zan kara jaddawa shine aiki ne na mai neman tallafi ya ja hankula sosai na alkalan da ke duba bukatarsa yadda za su nazarci bukatar su nemi tattaunawa sosai su fidda hukunci a tsanaki..

Idan aka gaza abubuwan da ke sama ana iya samun akasi.

Wannan makala ta bayyana a karon farko a shafin Eric Karsten personal website a 2016. An sake wallafawa a IJNet bayan neman izini.

Eric Karstens kwararre ne, mai taimakawa, mairubucin takardun neman tallafi , malamin kwaleji, edita, marubuci da ya shafi aiki, mai gyara harkokin kafafan yada labarai da tsare-tsare kan harkokin yada labarai a kafar intanet. Yana harkoki da suka shafi sama wa ‘yanjarida tallafi da aikin alkalancin takardun masu neman tallafi. Duka daga bangarorin masu neman tallafi da masu ba da tallafin. Da shirye-shiryen kafafan yada labarai a kasashe masu tasowa da kasashen Tsakiya da Gabashin Turai.

Main image CC-licensed by Unsplash via Olga DeLawrence.

 

⁠- Hadaddiyar Kungiyar Masu Bincike a Aikin Jarida daga kasashen duniya ce ta fara wallafa wannan labarin nan