Hanyoyi takwas (8) na kara yawan kudaden da ake bayarwa da Gift Ladders

Hanyoyi takwas (8) na kara yawan kudaden da ake bayarwa da Gift Ladders

Becky Chinn 6 ga watan Fabrairu, 2018

 

Tsokacin Edita: Ga kafofin yada labarai wadanda ba ruwansu da riba wadanda a ko da yaushe su ke neman tallafi, samar da hanyar samun kudade daga wurin jama’a ya na da mahimmanci. Ga shawara dangane da yadda za’a iya kirkiro a kuma gina kasuwa da abun da ake kira “gift ladder” da turanci — wato kayututtuka na kudi da yawa wadanda sukan fara da kadan har su kasance da yawan gaske. An fara wallafa wannan labarin ne a shafin Greater Public blog, wata kungiyar da ke da mazauninta a Amurka wadda ta shahara wajen taimakawa kafofin yada labarai si cimma burinsu ta hanyar tabbatar da dorewar makomar hanyoyin samun kudadensu.

Ko a yanar gizo ko ma a akwatin gidan waya, gift ladder ko kuma tsanin kyauta na daya daga cikin abubuwan da ake mayar da hankali wajen shiryawa kafin a kaddamar da neman kudi. Ko kuma ma a wasu lokuta tsanin kyautar shi ne kadai abun da ba’a sauya ba na tsawon shekaru masu yawan gaske. Amma kuma akwai dabarar da aka riga aka gwada na yadda ake bai wa mambobi karfin gwiwa su kara yawan kyautarsu daga lokaci zuwa lokaci.

Abun da aka fi la’akari da shi shi ne yadda aka tsara tsanin bayarwar da irin zabin da mutun ke da shi na irin mutanen ko kungiyoyin da za su rika bayarwar.

Ga dabaru takwas na gina tsaunukan bayarwar “gift ladders” masu inganci:

  1. Da yayyafi a kan cika rafi dan haka a fara da kadan.

Idan dai ba wai kuna mutane da yawa ba ne, ya kamata a fara tsanin da kyauta dan kan kani wanda daga nan za’a riga tafiya sama ana karawa. Ya na iya klasancewa daga hagu zuwa dama a kan yanar gizo ko kuma daga dama zuwa hagu.

  1. Ana iya bayar da zabi biyar ko kuma kasa da haka

A takaita yawan zabin da za’a bai wa duk wanda ke da niyyar bayar da tallafin. Idan tsanin ya fara da $25 zuwa $1,000 ko fiye, zabin ya yi yawa dan haka zai yi wahala mutane su bayar da wani abu. Amma idan ba yawa nan da nan mutun zai iya yanke hukunci kan abun da ya ke so ya bayar.

  1. A rika yi ana dubawa anan kuma gyara tsanin wadanda ke bayarwa a kai-a kai saboda a yi la’akari da makakin da su ka kai.

Ga misalin yadda ake yi yanzu:

Idan ba’a yi haka ba, wani na iya dawowa kasa ya rage yawan abun da ya ke bayarwa a maimakon ya tafi sama kamar dai yadda ya kamata a yi idan ana hawa tsani. Wannan haka ne domin yawan kudin da ake sa wa da farko ya kan kasance kasa da yawan da masu tallafi suka saba bayarwa. Ba za su sami sakon cewa ako kun su wane ne ba, amma wannan zai kara musu karfin gwiwa su cigaba da bayar da tallafi.

  1. Ku yi hattara kada a fara da kudi mai yawan gaske musamman idan mutanen da ba su taba yi ba a baya. 

Ko da a ce matsakaicin kudin da ake bayarwa kai tsaye kan kasance $100 wanda kuma ake turowa ta sakon gidan waya $50, za’a fi samun irin sakamakon da ake so idan aka fara sa kudin a kan misali $29 zuwa $35 daga nan sai a rika karawa a hankali. Na wata-wata kuma ana iya sanyawa a kan $5/kowani wata ko kuma $60 kowace shekara. Wannan ya taimakawa gidajen rediyo sosai wajen kara yawan mutanen da ke ba su tallafi.

Ka da ku manta, abin da ke da mahimmanci shi ne kara yawan mambobi ba wai samun kudi da yawa daga mutane kalilan ba.

  1. Za’a fi samun nasara wajen amfani sa salon tsanin watakila daga sakonnin da ake samu daga gidan waya a maimakon sake sabuntawa bisa la’akari da yadda mutane suka rika bayar da gudunmawa a baya.

Idan har za ku iya gwada na ku gidan rediyon, to ya kasance shi ne mafi mahimmanci a wajen ku. Idan ba za ku iya ba ku san da cewa akwai tashoshin da suka riga suka fara kuma suna amfani da irin wannan salon na tsanin. 

  1. Adadin kudin da aka sa ma ya kan yi tasiri

Yanzu da aka fara neman tsari mai dorewa yawancin tashoshi su kan sanya kudin da ba lallai ne sai an samu canji ba wai dan ya yi wa jama’a sauki misali kamar haka $60, $120, $240, $360… $5, 10, $20, $30. Musamman a yanar gizo, idan har kuna da damar gwada tsarin tsanin kafin ku fara amfani da shi, ku gwada da kudade kamar haka, $7, $12, $19, $29 da sauransu. Sanya irin wannan adadin mai yiwuwa zai ja ra’ayin jama’a su bayar da tallafi.

  1. Ku yi la’akari da abun da sauran kungiyoyin da ke kewaye da ku su ma suke yi.

Ku yi la’akari da kungiyoyin da kuke tallafawa dan ku ma ku ga abubuwan da suke yi dan ku yi koyi da su. Kuma a duniyar gizo-gizo ma ku duba shafukan masu ayyukan da suka shafi zamantakewa, da wadanda suke da wani buri mai mahimmancin da suke so su cimma wadanda kuma suke da magoya baya fiye da kafofin yada labaran gwamnati kuma dan haka suna da damar gudanar da gwaje-gwaje ta yadda za su iya gano abubuwan da suka fi tasiri su yi amfani da su.

Babu shakka akwai bukata yin taka  tsan-tsan wajen yin nazari, saboda wata sa’a abun da kuka samu gwaji ne kawai ba wai ainihin abun ba. Shi ya sa ya kamata ku rika sanya ido sosai kan baututwan ta yadda za ku iya zaben wanda ya fi dacewa.

  1. Ku duba irin saitin da aka yi manhajar da kuke amfani da shi wajen samun kudi

Wasu daga cikin su an riga an tsara su ta yadda za su fitar da bayanan da ake bukata ba tare da an tantance su ba. Dan haka idan ba an mayar da hankali an duba ba, akwai bayanan da za’a samu wadanda ba lallai su ne ake bukata ba.

Becky Chinn na daya daga cikin shugabanin LKA Fundraising & Communications (Samo kudi da Sadarwa). A baya ta kasance babbar darekta a na mambobi da talla a kafar yada labaran gwamnati a Oregon, Amurka.