Hanyoyi bakwai da kungiyoyi kanana da matsakaita ke takaita yadda suke samo kudade
Wallafar Armando Zumaya • Yuli 29, 2014
Na samu kaina ina duba manhajar WebMD a wayata samfurin iPhone suna da tsarin na iya duba me ke damun jikin dan Adam daki-daki da ba da shawarwari. Ko da yake akwai tari na gargadi wanda haka ya kamata ya kasance, kuma sannu a hankali na lura ina samun kai a yanayi na damuwa na cutar da nake dubawa. Na yi tunanin wannan manhaja yayin da nake tunanin rubuta wannan makala. Ina so na yi rubutu don mambobin kungiyoyi da ake kafawa ba don neman riba ba (kungiyoyi masu zaman kansu) da jagororinsu don su yi nazari su san matakin da kungiyoyinsu suke. ‘Tara kudi na lafiya, ba zai zama manhaja ‘yar kwalisa ba, afuwan, amma da shekarun da na yi 30 ina aikin samo kudade. (A lura: Samo kudade a lokuta da dama ana kiransu Ci gaba (Development) a harkar kungiyoyi da ake kafawa ba don samun riba ba.)
Na kasance mai samo kudade ba kamar kowa ba dalili kuwa shi ne na samo kudade ga kungiyoyi tun daga tushe har zuwa mataki irin na kwararrun masu bincike na Ivy League da ke ta’ammala da miliyoyi dubbai na Dalar Amurka. Na share shekarun aikina don neman samun “cikar buri” ta hanyar cike gibi wajen samar da kudade ga kungiyoyi na kasa, da jami’oi da asibitoci da sauransu inda muka yi fafutuka da samo tallafi daga daidaikun mutane da gidauniyar tallafi da sauran kamfanoni. Wadannan suna da kwararru da ma’aikata da aka tanada. Idan aka samu wani mai arziki wadannan cibiyoyi ke zuwa su same shi don neman tallafi. Sai dai kuma akwai kanana da matsakaitan kungiyoyi wadanda basa bunkasa duk da burin da suke da shi na yin hakan. Ko me ya jawom hakan?
Kanana da matsakaitan masana’antu na rige-rige zuwa gidauniyar tallafi guda daya {tilo} a duk shekara.
Idan ana magana ta kanana da matsakaitan masana’antu, Nagani babu tantama suna fama da matsalar kudin gudanarwa daga masu ba da tallafi dama rashin fahimtar aikin. Ba kawai kanana da matsakaitan kungiyoyi ba, koyon hanyoyi da dabaru na manyan cibiyoyi.
Magana ce ta sauya al’adar yadda ake neman tallafin kungiyoyi musamman daga daidaikun jama’a masu bayarwa.
Kanana da matsakaitan kungiyoyin na rige-rigen zuwa gidauniya shekara bayan shekara don samun kudadensu. Samun kudaden daga gidauniya ya fi sauki a fahimtarsu kasancewar babu bukatar a rika magana da mutum guda kan kudinsa.