Freelancing: Wuraren kai tayin labarai

Babu wasu wuraren da aka ware wa ‘yan jarida masu bincike mai zurfi su je su sayar da labaransu amma akwai wadansu shafuka da ke da amfani wajen tallafawa da shawarwari masu amfani.

Don samun kafar da za ta wallafa labarin da ya kunshi bincike mai zurfi, yawancin masu daukan rahotanni suna bayar da shawarar bi ta wata hanya ta daban, kamar yin bincike kan irin wuraren da za su dauki labarin da kuma tuntuban wani wanda ya san wani.

To sai dai akwai wadansu shafukan da ke bayar da damar yin tayi ga mutane da yawa sai kafafen su zabi wadanda su ke so (Ba’a cika yin haka wa rahotanni da ke bukatar bincike mai zurfi ba)

Ga ‘yan freelancing da ke yin bincike mai zurfi abin da ya fi mahimmanci shi ne su sami aikin da zai biya kananan bukatu yayin da suke neman babban labarinsu

Akwai shafuka da dama na samun ayyukan yi dan haka wanda mu ka tattara ba cikakke ba ne. Amma mun sanya wadansu manyan wurare masu mahimmanci amma kuma naku bincike zai iya ba ku abin da ya zo daidai da kwarewar ku da harshe da kuma yanki.

Journo Resources, wata kungiya mai zaman kanta a Burtaniya tana da wani jerin sunaye na irin kalmomin da za’a iya amfani da su wajen bincike a kafofin sadarwa na soshiyal mediya.

Wata hanya mai kyau it ace neman abokan aiki domin a yi aiki tare da su. Wasu daga cikin shafukan ana iya gano su ne kawai idan aka yi amfani da sunan yankin da ake so. Zai yi kyau a sami abokin aiki a wani yankin na daban.

Da duk wadannan a zuciya yanzu ga wadansu shafukan da ka iya taimakawa:

HackPack an yi shi ne dan ya taimakwa freelancers, kwararru da kafafen yada labarai a duniya. Kusan mambobi 10,000 daga kasashe 169 na biyan wani dan kudi dan yin rajista su nuna abubuwan da suke yi, harshen da suke amfani da shi, kwarewa da kuma lokutan da suke aiki. A nan mambobi suna iya ganin ayyuka da wasu damammaki wadanda za su iya nema su samu. HackPack na kuma shirya tarukan karawa juna sani.

Paydesk – wanda wani tsohon freelancer ya kirkiro dandali ne da ke hada ‘yan jarida da kafofin yada labarai a kasashen duniya ya kuma taimaka wajen ganin an biya su. A kan kira shi uber na ‘yan jarida. Burin paydesk shi ne taimakawa kafafen yada labarai amma kuma ‘yan jaridan da suka yi rajista suna iya rubuta tayi yadda editoci da produsas za su gani. Masu amfani da dandalin yawancin kamfanonin labaran Amurka da Burtaniya ne.

Pitchwiz – na da burin samar freelancers da editocin da za su dauki aikin su yayin da su kuma editocin ke neman freelancers. Rajista kyauta ne. Kuna iya neman “labaran da ake taya” ko kuma “irin labaran da ake so.” Shafin na taimakawa da sadarwa tsakanin wadanda suka yi rajista.

101Reporters – Wanda ke da mazaunin shi a Bengaluru India “Su kan dauko labarai daga ‘yan jarida a karkara a duk fadin kasar, sai su gyara su tallatawa manyan kafofin yada labarai na kasa da na kasa da kasa. A cewar shafinsu.

The Professional Freelancer, mai mazauni a Burtaniya na rubuta wasikun labarai. Ya kan bukaci wasu labarai na musamman. Ana iya biyan pounds 90 a shekara dan samun ra’ayoyin Anna Codrea-Rado.

The solutions Journalism Talent Network – a karkashin jagorancin wannan kungiyar, dandalin da ta samar na hada masu freelancing da editoci. Mutun zai cika form, ya sa duk bayanan shi sai a wallafa wa editoci su karanra

Inda ya kamata a koyi batun sanya farashi

 Shafuka da yawa na bayyana nawa kafofin yada labarai ke biya. Wadanda ke fada ba su cika bayyana sunayensu ba kuma wata sa’a bayanin ba daidai ba ne dan haka ya kamata a yi hattara.

The Freelancer wannan na da bayani kan albashin kafafin yada labarai sama da 100, wadanda suka yi bayanin bas u bayyana sunayensu ba. Yawancin kafodin na Amurka ne a ciki har da Haaretz, BBC da The Guardian.

Who Pays Writers? Wannan shafin ma kyauta ne inda mutane da yawa suka bayyana nawa ake biya, irin aikin, tsayin da ake bukata, tsawon lokacin da ake dauka kafin a biya da sauransu. An bayyana kafafe da dama a ciki har da wadanda ban a Amautka ba.

Asia Freelancers’ Info Sharing Sheet wannan sunayen kafofin yada labarai ne da yawan kudin da suke biya tare da lambobi da adireshin edita

Study Hall – Kasancewa mamba a nan kyauta ne kuma kungiya ce ta masu freelancing wadda ke bayar da kundin yawan albashi, listserv da sauransu.

Journo Resources –  wanda aka bayyana a can sama, yana da dogon jerin sunayen kafafen yada labarai da abin da suke buya.

Industrial Workers of the World Freelance Journalist Union – Yana da bayanai kan kudaden da yawancin kafafen yada labaran Amurka ke biya

Batun raba yawan kudin da kafofin yada labarai ke biya, batu ne da aka tattauna a 2020 a labarin da Elizabeth King ta rubuta a jaridar Columbia Journalism Review.

How Much Do Freelance Writers Really Get Paid (And How To Increase Your Rates) wani labarin da Alexander Cordova ya rubuta dangane da yawan kudin da kafofin yada labaran Amurka ke biya.

Wuraren Samun Aikin Rubutu Na Freelancing

Ko da yaush masu aikin freelance na kokarin neman hanyoyi masu hikima na samun ayyukan yi. Duk da cewa ba’a cika samun tallan da ke neman ‘yan jaridan da ke aikin bincike mai zurfi ba, ‘yan jaridan na cewa yin labarai na batutuwan yau da kullun na da mahimmanci sosai a gare su domin shi ne kadai hanyar samun abin dogaroo.

Jerin sunayen da ke kasa kadan ne daga cikin wuraren. Kuna iya karawa da shawarwarinku na irin wuraren da za’a kara idan kuna da shi a nan/here

Fiverr shafi ne da ke alfaharin cewa yana da ayyukan yi sama da 250 a fannoni daban-daban a ciki har da rubutu da bincike

Flexjobs yana da ayyuka daban-daban amma yana da ayyukan da suka shafi rubutu

The Freelancer – wannan na freelancers ne kuma burin shi, shi ne ya hada freelances da sana’o’in da ke bukatar kwarewarsu.

FreelanceWriting.com Yana da jerin sunayen wuraren samun aiki kullun

Guru – Akwai sashin rubutu da fassara

Indeed – na zargin cewa shafin shin a kan gaba a duniya wajen ayyukan da freelancers za su iya yi. Ga fannin “online freelance writer.”

Upwork – na da ayyukan da suka shafi rubutu daban-daban har da bincike a intanet da aikin jarida na freelancing inda ake samun aiki.

World Fixer Kungiyar sadarwa ce ta kasa da kasa wadda ke hada kafofin yada labarai da juna, amma kuma har da ‘yan kasuwa da jami’an gwamnati da kwararru wadanda za su iya kula da ayyukansu a kasashen waje.