Freelancing: Kariya da Tsaro ga ‘Yan Jarida

Freelancers yawanci sai dais u yi ta kansu idan ya zo batun tsaro. Tsaron kan su da ma na kayayyakin aikinsu musamman na dijital, amma akwai bayanai da dama da za su iya taimakawa. Akwai shafukan da suka hada da

Kariya da Tsaro

Tsaro a fannin dijital

Tsaro a fannin Shari’a

Agajin Gaggawa wa ‘yan Jarida

Aiki Da Wanda Ya Dauke ku Aiki

Matakin farko a matsayin dan jarida mai zaman kan shi, shi ne fahimtar abin da ya kamata kafar da ka ke ma aiki ya yi.

Wa ayyukan da ke da hadari wajibi ne a sayi inshore. Tambaya ko kuna cikin wanda kafar ta saya wa kanta. Idan kuna ciki ya yi kyau idan kuwa ba ku ciki ku nema.

Kayayyakin aiki da na’urorin sadarwa, da kayan sa wa na musamman.

ACOS Alliance tana da jerin abubuwan da ta ke ganin ya dace a tattauna da kafafen yada labarai.

Bayanai kan kariya da Tsaro 

A kasa, sashi ne da ya kunshi bayanai dangane da Tsaro daga kundin GIJN

Kwamitin Kare ‘Yan Jarida (CPJ) tana da bayanan da ta yi kashi hudu a 2018 wanda ta ke kira safety kit. Wannan na baiwa ‘yan jarida da dakunan labarai irin bayanan da suke bukata kan kariya na jiki, na dijital da na kwakwalwa a harsuna daban-daban.

CPJ tana kuma sabunta bayanan.

Mai mazauni a Landan, Gidauniyar Rory Peck na tallafawa ‘yan jarida da iyalansu a duk fadin duniya – tana daga mu su kiman su, kula da tsaro da jin dadinsu da kuma tallafa mu su su yi rahotannninsu cikin walwala da rashin fargaba ko tsoro.

Gidauniyar Tabbatar da Walwalar ‘Yan Jarida da ke da mazauninta a San Francisco ta wallafa wata jagora a 2020 na yadda ‘yan jarida za su iya aiki a gida ba tare da fargaban rashin tsaro ba. Jogarar ta mayar da hankali kan tsaro a fannin dijital

Reporters without borders su ma sun rubuta na su jagorar tare da hadin gwiwar UNESCO. Ana iya karantawa a Turanci, Faransanci, Spanianci da Portuganci

Abarji Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Bincike Mai Zurfi a Brazil sun rubuta jagora dangane da tsaro a lokacin zanga-zanga. Ita ma ana iya karantawa a Turanci, Portuganci da Spanianci

Shika-shikan kariya na masu freelancing wanda ACOS Alliance suka wallafa na bayani ne dangane da abubuwan da ya kamata a yi, dan tabbatar da tsaro a dakunan labarai.

COVID-19 News Organisations Safety Protocols: Wannan yana fadakar da masu dauko rahotanni da editoci kan yadda za su dauko rahotanni irin na annoba ba tare da sun janyo wa kansu wani hadari ba.

Frontline Freelance Register (FFR) wannan kungiya ce ta mambobi wadda ke birnin Landan “Kungiyar na bude wa duk ‘yan jaridan da ke fuskantar hadari a wurin aikin su wadanda kuma su ke bin ka’idojin mu.” Akwai mambobi kala biyu, na kyauta wadanda suke samun bayanai da wasikar labarai da dai wadansu kananan bayanai kamar idan za’a yi taro da sauransu. Akwai kuma wanda ake biyan kudi $75 wadannan suna samun wani kati na musamman kuma suna iya samun kwararrun shaidu idan suna neman wani abu, suna samun ragi da kuma inshora

FFR ta na kuma fitar da wani rahoto da ke bayan kan halin da freelancing ke ciki. Rahoton shekarar 2019 ta yi shi ne kan martani da bayanan da ta samu daga ‘yan jarida 380 daga kasashe 70. Daga cikin abubuwan da ta gano har gargadi ga ‘yan jaridan a duniya baki daya: “Idan ba’a biya freelancers a kan lokaci ba, za’a tilasta su neman hanyoyi marasa tsada domin su tabbatar da tsaron kansu tunda ba su da kudin hayan tasi mai kyau ko zama a otel din da ke bayar da ingantaccen tsaro ga baki ko kuma ma biyan kudin inshora dan zuwa filin daga.