Bincike Mai Zurfi a aikin Jarida: Yadda ake gabatar da tayin labarai

Image: Pexels

Tayin rahotannin da babu tabbas ko kuma suna dauke da batutuwa masu sarkakiya sun fi wahala saboda suna bukatar yarda tsakanin bangarorin biyu.

Bugu da kari, kudin da za’a kashe wajen yin irin binciken na da yawa, kuma ba lallai ne kwalliya ta biya kudin sabulu ba. Yana da wahala a iya kimanta lokaci da yawan aikin da za’a yi, dan haka da wuya a tantance ko yin binciken zai zama da wani amfani.

Daga karshe yana da hadari. ‘Yan jarida masu zaman kansu su kan fuskanci kalubale na musamman idan suna aiki kan labarai masu sarkakiya, akwai kuma hadaruka na lafiya da shari’a da kafar yada labaran ba za ta iya daukar nauyi ba.

Duk da haka, bincike mai zurfi a aikin jarida tsakanin ‘yan jarida masu zaman kansu na da karfi sosai. Ganin cewa suna da ‘yancin kansu da walwalar zaben labarin da suke so da inda suke so a buga, ‘yan jarida masu zaman kansu suna samun alheri sosai. Wasu sukan kulla dangantaka da editocin kafofin yada labarai wasu kuma su kan dauki kananan ayyuka a gefe dan toshe wasu kafofin, domin su bunkasa yawan aiki da albashi a matsayin marubuta, malamai ko kuma masu bayar da shawara.

GIJN ta duba irin kalubalen da ake fuskanta wajen sayar da labaran da aka yi mu su bincike mai zurfi ga kuma wadansu daga cikin shawarwarin da suka samu daga kwararru.

Zamu mayar da hankali a kan:

 • Neman kafafen tarayya
 • Gabatar da tayi mai kwari
 • Kare ra’ayoyi
 • Tantance kasafin kudin

Baya da wannan GIJN ta kuma hada wani jadawali na shawarwari da dabarun da za su taimkawa ‘yan jarida masu zaman kansu lokacin COVID-19.

Samun Kafofi

Akwai bukatar aminci da yarda tsakanin kafafen yada labarai da ‘yan jarida masu bincike mai zurfi dan haka ne ma yawanci ke son hulda da wanda suka riga suka sani.

Kulla dangantaka da labarai na yau da kullun daga farko ya fi domin farawa da irin labaran da ke bukatar bincike mai zurfi zai yi wahala,

Wata shawara kuma ita ce haduwa da editocin da ku ka san za su so labarin a irin manyan tarukan ‘yan jarida ko kuma taron karawa juna sani.

Yin Bincike

Lokacin bincike ka da ku duba kafofin da ke wallafa rahotannin bincike mai zurfi kadai, ku duba har da kafofin da ke da sha’awar batun da ku ke so ku rubuta a kai. Da wannan a hannu, kuna iya cigaba da binciken:

 • Karanta abin da suka taba rubutuwa dangane da batun a baya da ma sauran batutuwan da su ka yi rubutu a kai
 • Fahimci salon rubutunsu da irin matsayin da su ke dauka
 • Ku lakanci kudurinsu/manfofinsu
 • Duba manyan editocinsu
 • Tambaya ko ku kan ku ko wani da ku ka sani ya san wani a wurin ta yadda zai bude muku kofar shiga

Ku duba kasuwanni da dama dan sayar da labarin “ku yi amfani da duk wata dabara da kuka sani na neman labarai” kamar yadda Rowan Philip na GIJN ya kwatanta a kasidar da ya gabatar a GIJN 2019 mahawarar da aka yi kan freelancing.

“Ya kamata ’yan jarida masu zaman kansu wadanda ke bincike mai zurfi su rika samun kafofi da yawa na sayar da labaransu ma kowani labari da za su rubuta, idan har aikinsu zai dore,” ya rubuta, Rowan shi kan shi ya dade yana freelancing.

Wadanda suka kasance a mahawaran sun kwatanta kafofi da dama, a ciki har da Jarida, hotuna, da rediyo wanda zai kara yawan kudaden shiga.

Gabatar da tayin

Image: unDraw

Da zarar kun tantance wuraren da ku ke so ku wallafa rahotanninku sai ku shirya tayi.Yawancin hanyoyin da aka saba sayar da labaran yau da kullun ne ake amfani da su a labarin da zai bukaci bincike mai zurfi. Ya kamata tayin ya zama takaitacce kuma mai jan hankali. 

“Ya kamata ku ja ra’ayin edita ko duk wanda ke sauraro cewa ku ne ku ka dace ku yi wannan labarin saboda kuna da msaniya, majiyoyi da kwarewar da ake bukata da sauransu, ko kuma ka sami wasu takardun da ba kowa ke sane da sub a,” a cewar Catalina Lobi-Guerrero, wata ‘yar jarida mai zaman kanta a Columbia kuma tsohuwar editan GIJN wadda ke da shekaru sama da 10 na gogewa.

Shawarwari daga editoci

Editan jaridan The Atlantic Scott Stossel ya bayar da manyan shawarwarin shi a wata hirar da ya yi a 2017:

 • Ku dan fara rahoton ku tabbatar cewa kun yi tunanin yadda zai kasance
 • Ku cike duk wani gibi. Ku gano wadanda abin ya shafa, abubuwan da wadanne irin hadurruka za’a fuskanta kuma me ya sa labarin ke da mahimmanci
 • Ku nuna kwarewarku a rubutu. Tayin kan shi ya kasance kamar labari kuma ya gabatar da wata kusurwar da za’a fayyace.
 • Ku sami wani dan wasan kwaikwayo. A fayyace wasan kwaikwayon sosai a tayin
 • Fahimci mahimmancin labarin. Ku tabbata kun danganta shi da abin da ke faruwa a labarai
 • Ka da ya kasance tsohon labari

Bisa bayanan takardar jagorar bincike mai zurfi a aikin jarida, daya daga cikin shirye-shiryen Kafafen yada labarai na duniya na gidauniyar Konrad Adenauer. Duk wani tayi ya kasance yana da.

 • Takaitaccen labarin
 • Abin da ya sa labarin ya dace da jaridar ko wadanda ke karantawa
 • Gajeren bayani kan yadda za’a sami labarin da irin matakan da za’a dauka
 • Tsawonlokacin da zai dauka
 • Kasafin kudi

Sarah Blustain, babban editan Type Investigations ta shirya wata takardar shawarwari kan rubuta tayin da ke jaddada cewa ya kasance “takaitacce,” “kai tsaye,” “sa’annan ku baiwa editoci abin da su ke bukata su kai labarinku kan tsanin labaran kafofinsu,” a cewar ta yawanci ta na bayar da shawarar cewa tayin ya kunshi sakin layi hudu da mahimman abubuwa guda hudu:

 • Mene ne labarin
 • Me ya sa ya ke da mahimmanci – me ya sa ya ke da mahimmanci yanzu.
 • Me bincike ke nunawa
 • Me ya sa ku za ku rubuta

Mother Jones, wata kasidar Amurka da ke wallafa labaran bincike mai zurfi ta jaddada wadannan shawarwari a littafin da ake kira Freelance Writer Guidelines:

“Fada mana a sakin layi ‘yan kalilan abin da za ku rubuta a labarin, abin da ya sa ya ke da mahimmanci ko ban sha’awa, da kuma yadda za ku yi labarin. Ya kamata tayin ya nuna matsayin da za ku dauka, murya da salo. Ya kuma kamata ya amsa wadannan tambayoyin: Wani kwarewa ku ke da shi ku rubuta wannan labarin? Yaya dangantakarku ta ke da majiyoyin ku? Idan an riga an yi wasu labarai dangane da wannan batun, me zai banbanta na ku – ya inganta shi??

Ku rubuta kadan game da ku da biyu ko uku na ayyukan da ke ka taba yi.

Wannan labarin na kafar yada labaran Nieman ne da aka wallafa a 2018 – The Pitch: At the Guardian’s Long Read, No rigid formula or Greographic Limits – Ba kan bincike mai zurfi ne kadai ba kuma yana fadan gaskiya kan irin wahalar da ake sha. “Shawarar edita: Ku yi nazarin abun da aka wallafa a baya. Ku kwatanta cewa kun san abin da ku yi, ku kuma ja hankali.”

Duk da cewa an rubuta da burin neman tallafin kudi ne, wannan kasidar da Eric Karsten ya rubuta a 2016 mai taken How Not to Win Jornalism Grant, wato Yadda Bai Kamata a Sami Tallafin Aikin Jarida Ba, wanda GIJN ta sake wallafawa a 2018 na da shawarwari masu kyau.

Abin da Editoci Ke Nema a Tayi Kashi na biyu na jerin rubuce-rubuce a kan gabatar da tayi wa kungiyar hadin-kan Journalim Solutions a 2018, Julia Hotz ra fadada wadannan batutuwan guda takwas:

 1. Amsa mai gamsarwa dangane da tambayar “Me ya sa masu sauraro/karatu za su damu?”
 2. Alamar cewa kun yi bayar da labari kuma akwai labarin bayarwa
 3. Hujjoji – masu yawo ko masu inganci – dangane da tasirin da labarin zai yi
 4. La’akari da koma bayan da tasirin da kuma yadda za’a sanya ido a kai
 5. Takaitaccen bayani na yadda labarin zai fara da yadda komai zai tafi daga baya
 6. Bayanin kan yadda ka ku rawaito labarin da dalilin ya sa ku ne ku ka dace ku yi rahoton
 7. Kanun da zai talata mahimmancin labarin ya kuma nuna cewa labarin ba zai tsufa ba
 8. Fahimtar abin da kafar watsa labaran ke yi (da wanda ba ya yi)

Kashin farko na labarin na hade da wani labarin ne (companion piece) wanda ya tsokaci kan matakan farko na rubuta tayi, yayin da kashin karshe shi kuma ya kawo misalan taye-tayen da suka yi nasara.

Yadda ake nasarar yin tayi ga jaridar New York Times (ko wani) wanda Tim Herrera ya rubuta yana kunshe kurarai ukun da ‘yan jarida suka cika maimaitawa,” farawa da “Ba ku san mene ne labarin ku ba.”

Abin Da Ya Hana Daukar Tayin Ku – Daga Bakin Editocin Da Kansu – Shawarwari daga editocin manyan jaridu wadanda Ben Sledge ya yi hira da su.

One good list shawarwari ne na kafafen yada labarai dangane da irin abubuwan da suke so masu tayin rahotanni su kula da su,wanda kungiyar ‘yan jarida kwararru na Amurka ta wallafa.

Kafofin yada labaran da suka kunshi bincike mai zurfi na bukatar da yawa daga wurin dan jarida

Sjafukan kafafen yada bincike mai zurfi su kan bayyana irin abubuwan da su ke nema. Duk da cewa kusan ko wanne na da abin da ya ke so, akwai wasu batutuwan da su ka zo daya.

Reveal, gidan rediyon bincike mai zurfi na Amurka wanda ke karkashin jagorancin Cibiyar Labaran Bincike Mai Zurfi kan bukaci bayanai da yawa kuma su kan yi tambayoyi masu wuyan amsawa.

Takardar cikawa dan neman aikin da su ya fara kamar kowanne, yana fadawa ‘yan jarida cewa cikin kalmomi 500 su rubuta “kadan daga cikin abin da labarin zai kunsa da kuma tambayar da zai amsa.”

Akwai kuma wasu karin tambayoyin da suka hada da:

 • Su wa abin ya shafa?
 • Me ke sa labarin kasancewa abin da ya shafi kasa baki daya?
 • Me ya mayar da shi labari mai kayatarwa irin wanda za’a sa a rediyo?

Sai su kuma editocin na Reveal su ka cigaba da zurfafa tambayoyin su ka kara wasu guda tara wadanda su ka hada da:

 • Bayyana bayanai biyar da ku ka riga kuka samu ko kuma ku ke aikin samowa
 • Yi mana bayani kan wadanda abin ya shafa da irin wuraren da ku ke sa ran nadan bayanansu
 • Su wa suka taba yin wannan labarin (bamu adiresoshin intanet ko wata hujja) ta yaya na ku zai banbanta?
Fuskantar rashin tabbas

A kan iya fuskantar rashin tabbas idan labari bai kasance yadda aka zata ba tun farko, amma wannan bai kamata ya zama koma baya ba.

Lobo Guerrero ta ce: “Wata kila daya daga cikin hanyoyin yin tayin labarin bincike mai zurfi shi ne a bayyana cewa: Ga abin da na ke fatan samu, idan har na iya cimma wannan buri, amma ko ma ban samu ba, zai iya zama labari domin …… (ku bayana abin da ku ka shirya dama) ko abin da editoci ke kira karamin labari da babban labari.”

Wannan jagoran na 2015 Kungiyar Yan Jarida Masu Bincike Mai Zurfi a Yankin Balkan (BIRN) na da wasu sassa masu dimbin amfani wajen tantance labari da kwatanta abin da zai iya zama babban labari da wanda zai iya zama karami. Yana rubuce ne a turanci.

Abin da Ya Kamata a Cire?

Akwai matsala duk sadda mutun yake da babban labarin da ya ke so ya saida. Ta yaya mutun zai bayyana labarin cikin kariya ba tare da ya bayar da komai ba? Dole ne tayin ya kasance kai tsaye, amma kuma bai kamata a fadi abubuwa da yawa ta yadda za’a iya amfani da bangaren labarin a wani wuri ba.

Blustain na bayar da shawarar cewa: “Bai kamata ku rubuta abubuwa da yawa dangane da binciken da ku ka yi ku baiwa wata kafar da za ta iya baiwa na ta mai daukan rahotannin ya je ya yi labarin ba.” Ta yi gargadi sosai kan bayar da majiyoyi.

Idan har kun ga kamar kuna iya yarda da kafar ku sa a yi muku yarjejeniyar cewa ba za su fadawa kowa ba (NDA Non-disclosure agreement) ba dole ne sai an yi shi cikin wani babban turanci ba.

“Kafa (X) ta amince ba za ta wallafa binciken da ke kunshe a tayin da marubuci (X) ya yi ba tare da masaniyar shi ba.”

Samantha Sunne ce ta tsara wannan turancin. Sunne ‘yar jarida ce mai zaman kanta New Orleans, Louisiana, wadda ke wallafa wata wasikar labarai da ake kira Tools for Reporters.

“Watakila NDA ya yi yawa, ya danganci aikin,” ta ce a wani rubutun da ta yi a 2018. “Ba zan ce a yi haka wa kowani labari ba saboda na gwada da wani editan da ban taba aiki da shi ba, sai ya ki daukan labarin kawai.” Yanzu Sunne ta fadawa GIJN cewa tana aiki da mutanen da take ganin ba sai an kai ga neman irin wannan yardar ba.

Kwararru a wannan fanin sun ce abin da ko daya bai kamata ku bayyana ba su ne majiyoyi da bayanan da kuke da shi.

Sunne ta bayar da shawarar cewa hanyar sauki na samun tabbacin cewa ba za’a yi muku satar bayanai ba shi ne a ce su rubuta a email.

Ga ‘Yan Jarida masu zaman kansu da dama, yadda ce komai. Wadanda suka dade suna aiki da juna, ko daya ba suwa damuwa. Wadansu kafafen kuma suna bayar da mahimmanci ga kare hakkokin marubuta.

Type Investigations, misali, yana daukar matsayi na sirri:

“Mun dauki hakin kare labaranku da gaske; Ba zamu baiwa wani banda editocinmu da suka riga suka gani ba. Mun kuma fahimci cewa watakila labarinku na da batutuwa masu sarkakiya. Idan kuna shakkan tura manan bayanan ta email ku sanar da mu domin mu shirya hanyar ta daban dan karbar labarin cikin kariya.”

Calculating Costs

Image: UnDraw

Shirya kasafin kudi na da mahimmanci wajen tabbatar da yin riba a aikin jarida na sa kai.

Idan mutun ya riga ya san abubuwan da zai kashe wa kudi zai iya sanin farashin da zai sanya wa aiki ya kuma san sadda zai ce ba zai dauki aiki ba idan kudin da ake tayawa ya yi kankanta sosai.

“Bayan da na yi ‘yan shekaru ina yin bincike mai zurfi a matsayi na na ‘yar jarida mai zaman kanta, sai na kirkiro da salon da na ke kira ‘tiers’” a cewar Sunne.

Ma kowane tier, ta kwatanta irin himmar da za ta sanya wajen nemo ra’ayoyi; “Dalilin yin hakan na da sauku: ban so in yi komai da komai – Hira, samo bayani, kasha kudin tafiya – Idan har ba abin da zan samu. Idan har ban sami yarjejeniya ba ko kuma ba editan da ya dauki labarin zan ajiye.

Sauran ‘yan jaridan masu zaman kansu sun yarda: Ku zauna cikin shirin kin karbar ayyukan da ba su da riba.

Wani dalili na yin kasafin kudi kuma shi ne dan a iya sanin wuraren da za’a kashe kudin a kan kari kada a shiga matsala daga baya.

Emmanuel Freudenthal kwararren dan jarida mai zaman kan shi ya rubuta shawarwari 6 na yadda ‘yan jarida masu zaman kansu za su iya rayuwa lokacin babban taron GIJN na 11.