Bayanai a aikin Jarida

Bayanai a aikin Jarida

GIJN ta tattara bayanai ta shirya su ta yin amfani da bayanan da ta samu daga gudanar da bincike a aikin jarida.

Mun fara da abubuwan da za’a iya amfani da su wajen koyarwa, daga nan sai abubuwan da suka fi amfani. Mun jera su yadda za’a iya samun bayanan da ake so cikin sauki.

Aikin jaridan da ke mayar da hankalin kan bayanan da ake tattarowa daga yanar gizo batu ne da ke sauyawa kullun. Dan haka ne GIJN ke sabunta bayanan da ke shafukanta a kai-a kai.

A babban taron GIJN19 da ya gudana a birnin Hamburg, mahalarta sun saurari kasidar da aka yi wa taken “Aikin jaridan da ake yayi, daga masu amfani da na’urori masu illimi zuwa sabbin dabaru”, wanda Sarah Cohen daga jami’ar jihar Arizona, Brant Houston daga jami’Ar Illinois da kuma Jennifer LaFleur daga jami’ar Amirka suka gabatar.

Haka nan kuma, a taron na GIJC19, malamin da ke koyar da aikin jarida a jami’ar Columbia, farfesa Gianna ta tattauna kan aikin jarida mai samun lambar yabo da yadda suka yi: Shekarar matattu, kiwon lafiya da miyagun laifuka.

Domin samun Karin bayani dangane da aikin jaridan da ke mai da fifiko kan bayanai, a duba wadannan littattafan da jagorori a wannan fannin daga ko’ina a duniya suka rubuta, wadanda da yawa daga cikin litattafan kyauta ne a yanar gizo.

Ayyukan da suka yi fice wajen aiki da bayanai a aikin jarida (wanda aka wallafa 2017) na dauke da shawarwari da dakunan labaran da ke fara amfani da data journalism za su iya amfani da shi. Kuang Keng Kuek Ser ne ya rubuta wa gidauniyar zuba jari domin bunkasa kafafofin yada labarai.

The Curious Journalist’s Guide to Data Journalism – Jagorar dan jarida mai neman zurfafa fahimtar data journalism (2016), wanda dan jarida mazaunin Amirka Jonathan Stray ya rubuta ya bayar da kyakyawar bayani kan yadda ya kamata a rika tunanin bayanai: “Wannan ba “yadda ya kamata a yi amfani da bayanai ba ne,” illa “Yadda bayanai ke aiki.””

Data for Journalists- Bayanai dan ‘yan Jarida: Jagora wajen rubuta rahotanni tare da tallafin na’ura mai kwakwalwa, (Karo na 5, 2018) farfesa a fannin jarida Brant Houston ya rubuta. Wannan na kunshe da bayanai daki-daki  kan yadda ya kamata a yi nazarin bayanai. Yana ma hade da misalan da za’a iya amfani da su wajen ganin salon nazarin a zahiri. (Akwai na saidawa ga mai sha’awa)

The Data Journalism Handbook 2 (2019) Littafin Jagora na Bayanai dan aikin Jarida. An yi bita an fadada wannan ne daga Littafin jagora na farko wanda aka wallafa a 2012. Litattafan biyu suna bayar da mahimman kanu dangane da da bayanai na aikin jarida. Jonathan Gray da Liliana Bounegru ne editocin da suka yi aiki a kai daga Public Data Lab. Editocin sun sami gudunmawar kasidu daga jagorori a fanin bayanan wadanda ke nahiyar Turai. Ana iya karantawa a harsuna da dama wadanda suka hada da Arabic, Azerbaijan, Chinese, Turanci, Faransanci, Girkanci, Japanianci, Rashanci, Spanianci da Ukranianci.

The Data Journalist (2017) Dan jarida mai amfani da bayanai: Wannan yana bayar da gabatarwa mai kyau daga manyan ‘yan jaridan Canada guda biyum Fred Vallace-Jones da David McKie. Akwai darussa a yanar gizo. (Duk mai sha’awa na iya saye ta hanyar yanar gizo)

Data Literacy: A User’s Guide – Illimin Bayanai: Jagorar Mai Amfani da Bayanan (2015) babban farfesan illimin jarida mazaunin Amirka, David Herzog ya yi bayani daki-daki dangane da hanyoyin amfani da bayanai. Herzog ya ma hada har da hanyoyin samun bayanan, yadda ya kamata a tantance, a tsabtace a kuma yi nazarin su.” (su ma ana iya saye)

Facts are sacred – Bayanan Gaskiya na da tsarki – tsohon ma’aikacin jaridar The Guardian Simon Rogers ya rubuta, inda ya bayar da kyawawan misalai daga bayanan da ke taskar blog din The Guardian.

Getting Started with Data Journalism – Fara amfani da Data Journalism (2016) ‘yar jarida mai zama a Burtaniya Claire Miller ta bayar da shawarwari masu taimakon gaske dangane da batun musamman wajen samun irin bayanan da ake bukata, tsabatace su da kuma gano labaran da ke cikin bayanan. (Ana iya saye)

How to Lie with Statistics –  Yadda ake Karya da Alkaluma – Wannan littafin wanda Darrel Huff ya rubuta kyakyawar misali ne na yadda za’a iya yin kuskure wajen amfani da alkaluma a cikin labarai. An fara wallafa wannan littafin ne a 1954 amma har yau ana koyi da darussan da ya gabatar. (Ana iya saye)

John Allen PaulosMalami ko kuma farfesa a jami’ar Temple ya rubuta litattafai da dama ya kuma yi sharhi kan amfani da alkaluma a al’umma da labarai. (Ana iya saye)

Numbers in The Newsroom – Alkaluma a dakin labarai (2014) Littafi ne mai amfani wajen rubutu da kuma amfani da alkaluma daga jerin litattafai masu bai wa editoci da masu dauko rahotanni bayani dangane da bincike a aikin jarida. ‘Yar jarida Sarah Cohen wadda ke zama a Amirka ce ta rubuta. Duk wani mai amfani da alkaluma wajen rubuta labarai da rahotanni yana bukatar wannan littafin.

Precision Journalism: a Reporter’s introduction to Social Science Methods/ Aikin jarida mai daidaito : gabatar da mai daukan rahotanni ga hanyoyin illimin zamantakewa (2002). Duk wanda ke sha’awan shiga Data Journalism na bukatar wannan littafin. Daya daga cikin wadanda suka yi jagora wajen amfani da alkaluma da illimin zamantakewa wajen kawo rahotanni, Philip Meyer ne ya rubuta wannan. An ma kaddamar da lambar yabo a sunan mazaunin Amirkan, dan karrama masu dauko rahotanni wadanda ke bincike mai zurfi a aikin jarida da editoci masu amfani da bayanai (musamman alkaluma)

Wadannan bayanai na kyauta za su taimakawa duk wanda ke fara aiki da irin wadannan bayanan a karon farko.

Jagora na hadin gwiwa wajen Data Journalism: Wannan littafin shawarwarin da ProPublica ta wallafa a 2019 ya duba batutuwan da suka hada da:

  • Ire-iren hadin gwiwar da za’a iya yi a dakunan labarai da yadda ya kamata a fara
  • Yadda ake hadin gwiwar da ya shafi bayanan da aka tattaro daga sassa daban-daban
  • Tambayoyin da suka dace a yi kafin a fara hadaka dan amfani da bayanan da aka samu daga wurare daban-daban
  • Yadda ya kamata a yi hadin –kai da bayanan da bangarori biyu ko fiye za su raba
  • Hanyoyin girkawa da kuma tafiyar da ayyukan da suka shafi bayanan

Data Journalism: MaryJo Webster’s Training Materials – Kayayyakin Horaswar da MaryJo Webster ta kirkiro ya kunshi kasidun da za su taimakawa duk wanda ke fara aiki da bayanai, wadanda suka hada da shawarwari, jerin sunayen litattafan da za su taimaka wajen inganta fahimta, umurni dangane da R, SQL, da alkaluma, da ra’ayoyin labarai. MarJo Webster ‘yar jarida ce da ke aiki da Minnesota Star-Tribune a Amurka.

Structuring and Sharing Data Investigations/ Tsarawa da raba binciken bayanai, wanda Marcel Pauly da Patrick Stotz daga jaridar Der Speigek na Jamus suka rubuta wa babban taron GIJN a shekarar 2019.

Data Editorial Process/Hanyoyin amfani da bayanai wanda Emilia Diaz-Struck daga Hadin gwiwar kasa da kasa na ‘yan jarida masu bincike mai zurfi ta rubutawa babban taron GIJC 2019

How to do #ddj With a Small Newsroom and a Limited Budget/ Hanyoyin amfani da #ddj a kananan dakunan labarai da karamin karfi kasida ce mai cike da shawarwari masu amfani wanda Pinar Dag ta gabatar a GIJC19 daga datajournalismturkey.

Glossary of Statistical Terms for Beginners – Jaddawalin kalmomin da ake amfani da su wajen rubutu kan bayanan da suka shafi alakaluma wanda iMedLab ya shirya.

Reverse Engineering Step by Step/ Hanyar fayyace bayanai ta yin amfani da dabarar Reverse Engineering ko kuma yin amfani da manhajoji dan komawa baya wanda Felix Ebert da Vanessa Wörmer na Süddeutsche Zeitung, Thorsten Holz na jami’ar Ruhr da ke Bochum a Jamus da Hakan Tanriverdi daga Bayerische Rundfunk (Rediyo) suka shirya wa GIJC19.

Data Journalism Tools/ Kayayyakin gudanar da aikin data Journalism daga shirin aikin jaridar kimiyya na Knights da ke jami’ar MIT. Wannan ya hada da jerin litattafai, manayan taruka, kayayyaki da sunayen ‘yan jaridan da suka kware wajen aiki da bayanai.

How to: Plan a journalism project that needs data entry/ Yadda ake tsara shirin jaridan da ke bukatar bayanai – Labari ne da Paul Bradshaw ya wallafa shafin ‘yan jarida

Diving Into Data Journalism/ Shiga aikin amfani da Bayanai a Aikin Jarida (2016) Samantha Sunne ta rubutawa kungiyar API. Wannan na kunshe da shawarwari da kuma ginshikan fara amfani da shi a dakunan labarai da ma irin kalubalen da za’a iya fiskanta wajen yin hakan.

Introduction to Data Journalism/Gabatarwa ga Data Journalism – manhaja ce ko kuma taswirar da dan jaridan Amurka Peter Aldhous ya rubuta domin karantarwa a jami’ar Berkeley. Yana dauke da darussa kan alkaluma, yadda ake samu a tsabtace da kuma amfani da manhajan lissafi wato spreadsheet da kuma irin zane-zanen da za su taimaki jama’a wajen fahimta.

Data Journalism: A guide for editors/ Bayanai dan aikin jarida: Jagora ga editoci Wannan labarin wanda Maud Beelman da Jennifer Lafleur suka rubuta kuma aka wallafa a 2019 na da taken “Gyara labaran bincike kan shi na da na shi kalubalen, musamman idan mutum bai saba da hanyoyin samun bayanan ba.”

A shekarar 2019, karidar the New York Times ta wallafa irin abubuwan da su ke amfani da su a dakunan labaransu dan inganta illimi kan bayanai. 

In Data Journalism, Tech Matters Less Than the People/ A aikin jaridan da ya fi mayar da hankali kan amfani da bayanai, fasaha ta fi mutane mahimmanci. Ben Casselman wani mai daukan labaran da suka mayar da hankali kan tattalin a jaridar New York Times, ya na amfani da wani salon da ake kira harshen fasaha mai suna R kuma yana aiki da bayanai masu dimbim yawa. Sai dai a wani labarin da ya rubuta a 2019 ya ce idan dai rahoto mai kayatarwa ake so a rubuta babu majiyar da ta fi yin hira da jama’a dan samun bayanai.

Quick Guide to Data Journalism/ Takaitacciyar jagora ga amfani da bayanai a aikin jarida wanda DataCamp ya rubuta ya bayar da ma’anar amfani da bayanai a aikin jarida, ya bayar da shawarwari kan irin harsuna ko kuma fasohohin da suka fi dacewa a koya da wuraren samun litattafai shafukan Tiwita da suaransu

Ricochet wanda Chrys Wu ya rubuta na da shawarwari da kasidu daga shekara da shekaru na zuwa manyan tarukan IRE da NICAR. Akwai shawarwari da dama har ma da misalai.

Data Journalism Archives/ Ajiyan bayanan aikin jarida Wannan rubuce-rubuce ne da yawa daga shafin Better News wadanda Cibiyar ‘Yan jaridan Amurka wato American Press Institute da Knight Temple Lenfest News Initiative suka dauki nauyi.

Wadannan manyan tarukan su na iya bayar da damar haduwa da kuma ma’amala da irin mutanen da ba ko da yaushe ne za’a iya haduwa da su ba, yana iya bayar da damar koyon sabbin dabaru da kuma tattauna mahimman batutuwa da sauran ‘yan uwa ‘yan jarida.

Cibiyar binicike mai zurfi a aikin jarida ko kuma Centre for Investigative Journalism a turance na da taron da ta ke yi a lokacin bazara, summer conference inda ta kan koyar da amfani da bayanai a aikin jarida a karkashin jagorancin manyan malaman da suka shahara a wannan fannin.

Data Harvest/ Girbin Bayanai – wani taro ne da ke gudanarwa daura da babban taron ‘yan jarida masu bincike mai zurfi a Turai. Za’a gudanar da mai zuwa daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Mayun 2022, a Mechelen da ke kasar Beljiyam.

European Data and Computational Journalism Conference/Babban taron Turai kan bayanai a aikin jaridayana kawo ma’aikata daga masana’antan da ‘yan jarida da kuma kwararru a fanin illimi

The international Journalism Festival/Bukin ‘Yan Jarida na kasa da kasa a Perugia na kasar Italy, inda a kan hada har da makarantar koyon amfani da bayanai.

Investigative Reporters and Editors/Masu daukan rahotanni da editoci a bincike mai zurfi wanda akan yi kowace shekara na mayar da hankali ne dungun kan  bayanai da bincike mai zurfi a aikin jarida

NICAR, shiri na masu daukan rahotanni da editoci masu gudanar da bincike mai zurfi kan dauki nauyin bakin babban taro kowace shekarar kan bayanai a aikin jarida da kuma koyarwa. NICAR kuma ta na da wani jaddawali ko kuma NICAR-L inda take samun shawarwari daga sauran ‘yan jarida. Tana kuma da shi a harshen Spanianci.

NODA, – Wannan babban taro ne na kasashen da ke yankin Scandanavia wanda ake kira Nordic Data Journalism a turance wanda kuma ya ke bajekolin fitattun ayyukan da suka fito yankin dangane da bayanai a aikin jarida. Wannan ya hada da labarai da hotuna da kuma lambobin yabo.

Akwai mai neman hanyoyin inganta illimi a fannin alakluma da lissafi? Wadannan shafukan suna koyar da jama’a kyauta ko kuma a farashi mai rahusa. Kuma akwai darussan a hotunan bidiyo dangane da batutuwa daban-daban da harsuna ma haka.

Kuna iya duba shafin GIJN a Youtube domin samun irin wadannan darussan kyauta.

Code Academy/Makarantar Code  Wannan na bayar da darussa kyauta da kuma farashi mai rahusa a darussan da suka hada da Python, SQL, PHP, C++, R, Java da sauransu. Akwai kuma zabin kasancewa mamba inda za’a rika biyan $20/wata-wata amma za’a dauka kudin shekara guda a tashi daya. Da wannan kudin mutun zai ci moriyar samun kwasa-kwasai daban-daban.

Cousera na bayar da darussa kyauta, ga wadanda kuma ke neman kwarewa ta musamman a wasu fannonin (Mutun na iya biyan $49/Kowace wata) a kimiyyar bayanai, alkaluma da kuma fasahohin shirye-shirye ko kuma programming language daban-daban a jami’o’i daga kusan duk kaasashen duniya. Ana gabatar da darussan a harsunan da suka hada da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci, Jamusanci da wasu da dama.

Datawrapper: Kayayyakin gudanar da taron karawa juna sani.

edX na bayar da darussa kyauta a yanar gizo wajen tsara shiri, nazarin bayanai da alkaluma shi ma a harsuna da yawa, a ciki har da Turanci, Spanianci, Chinese, Rashanci, Faransanci da Jamusanci. Dalubai kuma suna da zabin biyan $99 dan samun takardar shaidar kammala karatu.

Investigative Reporters and Editors/ masu daukan rahoto da editoci masu bincike mai zurfi suna horaswa ta yanar gizo

Google News Initiative/ Dandalin Samar da Labarai na Google –  na baiwa ‘yan jarida kayan koyon aiki, kuma sun fi mayar da hankali kan makaman aiki da google wajen samun bayanan da ake amfani da su a aikin jarida

Khan Academy/ Makarantar Khan na bayar da darussa kyauta a cikin hotunan bidiyo a yanr gizo inda suke koyarwa kai tsaye dangane da HTML, CSS, JS da SQL Languages

MIT Open Courseware tana bayar da darussa kyauta a Python, Java, da MATLAB. Kowani darasi na darasi cikin bidiyo da kuma ayyukan yi a gida.

Poynter’s News University – ta na bayar da darussa a bidiyo da kuma wadanda duk mai sha’awa zai iya yi a lokacin da yak e so. Batutuwan da ake koyarwa sun hada da nazarin bayanai, bincike mai zurfi a aikin jarida, da’a da kuma hanyoyin bayar da labarai. Yawancin darussan na bukatar biya amma akwai wadanda ba sai an biya kudi ba.

ProPublica ta wallafa darussa a YouTube dangane da batutuwan da suka shafi bayanai misali akwai gabatarwa ga code, yadda shafuka ke aiki, HTML, Basic CSS da CSS.

Workbench TrainingSuna bayar da darussa kyauta kan amfani da manhajan lissafi da yin nazarin alkaluma domin amgani da su wajen rubuta labarai ko rahotanni

The Investigative Journalism Education Consortium/ Hadin gwiwar BIncike mai Zurfi da illimi a aikin jarida na da wata hadaddiyar manhaja daga masu koyar da bayanai a aikin jarida. Shafin IJEC na kunshe da abubuwa makamantan wannan har ma da misalan irin bayanan da za’a iya amfani da su wajen koyarwa.

Scraping kalma ce ta turanci da ke nufin amfni da wata fasaha wajen tsara shirin da zai iya gano bayanan da ake nema ya kuma dauko su daga shafukan da ke yanar gizo. Ga wasi daga  cikin hanyoyin da za’a iya amfani da su wajen samo bayanai daga shafuka ko da kuwa illimin mutun a wannan fanni kalilan ne.

Wannan chapter/babin daga cikin littafin shawarwari dangane da bayan aikin jarida na daya wato The Data Journalism Handbook 1 na da shawrwari kan scraping da ma misalai.

Journocode (2019) Yan a bayar da bayanai a takaice dangane da scraping ko kuma neman bayanai. Wata kungiyar ‘yan jarida da kwararru a fannin fasaha a Jamus ne su ka hada shi.

Samantha Sunne ta bayyana ginshikan scraping a cikin wannan kasidar/presentation da ta gabatar. Yana kuma dauke da wsu adiresoshin shafukan da za’a iya samun karin bayani kan wuraren da za’a iya fara scraping, musamman ga wadanda suka kasance sabin shiga wajen amfani da wannan salon.

Mahukuntan gwamnati yawancin sun a da hanyar da ke taimakawa ‘yan jarida da ma al’umma baki daya wajen samun bayanai. Daga kasa, akwai kadan daga cikin wasu batutuwan da za su taimaka wajen fahimtar dokokin da su ka shafi bayanan gwamnati a inda ku ke, da ma yadda za su taimaka mu ku wajen rubuta wasikun neman bayanan,

The National Freedom of Information Coalition ko kuma Hadakar ‘Yancin samun bayanai na kasa, wata kungiya mai zaman kanta ne a Amurka da ke da shawarwari dangane da Dokokin ‘Yancin Samun Bayanai na Kasa da Kasa wanda aka fi sani da FOI a shafin su tare da bayanai kan dokokin kwace jiha.

Reporters Committee for Freedom of the Press/ Kwamitin masu daukan labarai dangane da ‘yancin walwalar ‘yan jaridaBudaddiyar jagorar gwamnati (An sabunta 2019) na dauke da bayanai daki-daki dangane da dokokin da suka tanadar da walwalar samun bayanai zuwa rukunnai daban-daban wadanda suka hada da wanda zai iya neman bayanan da suke samun goyon bayan dokar ta FOI abun da ake kira bayanan gwamnati, yadda ake daukaka korafi da sauransu. Wannan kuma ya hada da bayanan da suka danganci samun irin bayanan da aka ajiye a yanar gizo.

Society for Professional Journalists FOI for Pros/ Kungiyar kwararrun ‘yan Jarida Wadannan suna fayyace yadda ake neman bayanai bisa tanadin FOI, daga fahimtar dokar da ake amfani da ita, zuwa irin kalmomin da za’a yi amfani da su da kuma yadda za’a daukaka korafi ko da an hana mutun samun bayanan da ya bukata.

How to get a faster FOIA response/Hanyoyin samun amsa ga bukatar FOIA da gaggawa – 

Shawarwarin samun amsa daga mahukuntan da ba za su amsa tambayar ga na samun bayanai ba. Muckrock su ka rubuta

Da zarar aka sami bayanai, ana iya duba wadannan shawarwarin na kyauta da darussan da ke tsokaci kan yadda za’a iya bincike a kuma tsabtace su kafin a fara yin nazarin su.

Wannan labarin kyakyawar misali ce na abubuwan da ya dace mutun ya yi idan akwai gurabe a bayanan da mahukunta suka bayar (2021).

Data Biographies: How to Get to Know Your Data/ Hanyoyin gano tarihin bayanai (2017) taskar blog ce da Heather Krause ke rubutawa. Krause tana tare da shafin bai wa ‘yan jarida shawarwari dangane da bayanan aikin jarida a Canada mai suna idataassist wanda ke bayanai kan hanyoyin bincike da kuma tara bayanan (har ma da irin abubuwan da ke bayar da alamun samun kalubale nan gaba) na bayanai tun kafin a fara nazarin su.

The Quartz Guide to Bada Data/ Jagorar Quartz wajen gane gurbatattun bayanai (2018)

Wannan fayil ne a kan GitHub wanda ke tattauna irin matsalolin da aka fi gani a cikin bayanai da hanyoyin gyarawa. An fassara shi ziwa harsunan Chinese, Japanese, Portuganci da Spanianci.

ProPublica’s Guide to Bulltetproofing Data/ Shawarar ProPublica kan hanyoyin inganta tsaron bayanai (Updated 2018) Jennifer Lafleur ta hada tare da tallafi mai dimbin yawan da ta samu. Fitattun hanyoyin tantance bayanai. Har yanzu ana kan ingantawa dan haka kuna iya karawa da na ku shawarwarin

Wannan tutorial/darasin wanda dan jaridan Beljiyam Stijn Debrouwere ya hada yana bayani ne kan irin kurakuran da ake yawan samu a bayanai da kuma yadda za’a kaucewa yi mu su fassarar da ba dai-dai ba. Ana iya samun shi kyauta a shafin datajournalism.com.

Get started with OpenRefine/ Yadda ake amfani da fasahar OpenRefine (2017) Wannan darasin takaitacce ne inda ake amfani da hotuna a bayyana yadda ake amfani da fsahar tantance bayanan da ake kira OpenRefine. Wata malama a jami’ar UCLA mai suna Miriam Posner ta krikiro.

Cleaning Data in OpenRefine/ Tsabtacewa ko tantance bayanai a OpenRefine (2018) Wannan cikakken jagora ne tare da misalai da darussa cikin bidiyo wanda ke kwatanta yadda ake sarrafa bayanai idan ana amfani da OpenRefine. John Little ne ya kirkiro wannan. Little kwararre ne a kimiyan bayanai wanda ke aiki a dakin litattafan jami’ar Duke.

Wannan tutorial/darasin wanda dan jaridan Beljiyam Maarten Lambrechts ya koyar gabatarwa ne ga amfani da manhajan Excel dan tantance bayanai da kuma tsabtace su yadda za’a iya ganewa cikin sauki. Wannan koyarwar na bukatar rajista amma ba’a biya. Ana iya samun shi a kan shafin datajournalism.com.

Akwai bayanan da ba su da kan gado? Wadannan manhajojin za su taimaka muku wajen sarrafa su ta yadda za ku iya amfani da su a saukake.

OpenRefine – Wannan manhaja ce ta kyauta wadda ake amfani da ita wajen samo bayanai, gyarawa da kuma tsara su yadda za su yi amfani. Yana da mahimmanci sosai musamman idan akwai bayanai da yawa wadanda aka samo su a birkice. Akwai shi a harsunan Ingilishi, Chinese, Spanianci, Faransanci, Rashanci, Potuganci (wanda ake amfani da shi a Brazil), Jamusanci, harshen kasar Hungary, Ibranianci, harshen kasar Philippines, Cebuano, da Tagalog. Ana iya samun darasi mai kyau a nan/here.

 

Samun bayanai daga fayil na PDF abu ne da ‘yan jarida da dama ba su son yi. To amma akwai manhyjoji na kyauta da dama da za su iya taimakawa da wannan daikin. Tabula wannan yana taimakawa wajen samun bayanan da aka jera su cikin rukunnan da aka zana. Wata kuma it ace XPDF wadda take tallafawa bayanai a wasu harsunan da ba turanci ba. CometDocs wannan na da shafukan kyauta amma kuma akwai wanda ake biya wanda zai bai wa mutun wurin ajiya mai girma dan ajiye manyan bayanai.

CSVKit wannan na taimakawa wajen juya bayanai da kuma aiki da CSV dan yin amfani da bayanan da aka zana.

Workbench wannan makaman aiki ne da ake amfani da su wajen samo bayanai, tantancewa da tsabtacewa kafin a yi nazarinsu. An samo wannan ne daga makarantan koyon aikin jaridar Columbia wato Columbia’s School of Journalism.

Yawancin lokuta manhajar lissafi ce makamar aiki na farko da ‘yan jarida kan koyi amfani da shi. Wannan na da mahimmanci waken tsabacewa da kuma yin nazarin bayanai. Microsoft Excel da Google Spreadsheets ne aka fi amfani da su. A kasa mun yi muku tanadi wadansu manhajojin da su ma za su taimaka muku wajen inganta fahimtanku na aiki da wadannan manhajoji

Data Journalism Training: Beginner Excel/Horaswa kan bayanai dan aikin jarida Wannan darasi ne da MaryJo Webster ta shirya wanda ke bayyana yadda ake shirya bayanan da za’a yi amfani da su a Excel. Ta kuma nuna wadansu daga cikin fasahohin da ake amfani da su cikin hotuna. Wannan darasin zai fi amfani ga wadanda suka amfani da babban Komfutar da ke kan teburi.

Cousera and edX su ma suna bayar da darussa kyauta a bidiyo akwai Excel domin kasuwanci, nazarin bayanai da sauransu, wadannan ba lallai dan aikin jarida ba ne amma kuma suna iya koyar da makaman aikin da za’a iya amfani da su wajen gudanar da aikin jarida.

Finding stories in spreadsheets/ Samo labarai cikin alkaluma ko manhajan lissafi (2016) Wanda dan jarida Paul Bradshaw ya rubuta yana bayar da bayani dalla-dalla ga ‘yan jaridan da ke neman fara aiki da irin wadannan bayanan. Yana bayar da shawarwari kan yadda dan jarida zai gane mene ne labari a cikin alkaluman da ke gabansa. (Ana iya saye)

GFCGlobalYa na gabatar da darussa kyauta kan manhajan lissafi na Excel inda yak e duba batutuwan da suka hada da gyarawa, da hotuna. Akwai jarabawa a karshen darasin

Mr ExcelDuk wata amsar da ake nema dangane da manhajan lissafi na Excel ana iya samu a nan. Bill Jelen ya na da shawarwari da dama tunda tun 1998 ya ke tara bayanai dangane da shi.

A Reporter’s Guide to Excel/Jagorar masu dauko rahotanni kan Excel (2016) Wannan na bayar da bayanai daki-daki tare da hotuna na yadda ake amfani da Excel a aikin jarida musamman yadda ake tsabtace alkaluma. Akwai kuma misalai wadanda za’a iya amfani da su wajen koyo.

Spreadsheets for Journalism/ manhajan lissafi dan aikin jarida (2019) Wannan takaitaccen bayani ne wanda dan jarida mazsaunin Amurka Brant Houstan ya rubuta dangane da yadda ake amfani da Excel wajen yin nazarin bayanai da alakaluma. Ya bayyana abubuwan da su ka fi dacewa da Excel da kuma yadda ake yin lissafi da shi.

Ana yawan amfani da SQL idan ana aiki da manhajojin ajiye bayanai. Yana da mahimmancin gaske a lokutan da ake amfani da bayanai masu yawan gaske wadanda Excel ba zai iya dazka ba domin yana iya hada bayanai daban-daban ya yi nazarinsu. Ana amfani da irinsu da dama a dakunan labarai, wadanda su ka hada da Postgresql da DB Browser SQLite.

Ga wasu shawarwari kan yadda za’a iya amfani da su.

Ga wata kasida mai kashi kashi uku kan yadda ake amfani da QL, an gabatar da kasidar yayin babban taron GIJN 2019. Jodi Upton daga jami’ar Syracuse da ‘yar jarida mai bincike mai zurfi Crina Boros da Helena Bengtsson daga gidan talbijin na Sveriges da ke Sweden su ka ributa. SQL (Part 1),SQL (Part 2), SQL (Part 3).

Excel to SQL Crosswalk (2017) wanda MaryJo Webster ta rubuta bayanai ne da ke nuna kamanceceniyar da ke tsakanin Excel da SQL dan ‘yan jaridan da ke so su fara amfani da SQL kuma sun riga sun dan san wani abu a kan Excel.

Introduction to SQL for Data Journalism/ Gabatarwa ga SQL ga masu amfani da bayanai dan aikin jarida (2014) wannan wani bangare ne na manhajan koyarwar a ajin Dan Nguyen, a jami’ar Stanford. Ya bayar da bayanai dangane da SQL, ta yin amfani da hotunan shafukan, misalai na koyo da adiresoshin shafuka da kuma amsoshi ga tambayoyin da aka fi yi. Ya kuma kara da wasu darussan da ke bayani a kan abubuwan da suka fi wannan wahala.

Khan Academy/ Makarantar Khan Ya na da darassin da ke bayar da gabatarwa ga SQL, darassin na cikin bidiyo kuma ya na bayar da bayanai daga mafi sauki zuwa mafi wahala.

Practical SQL (2018) wanda Anthony De Barros ya rubuta, bayanai ne dangane da manhajojin SQL da wadanda suka fi shi. Amma an yi bayanan yadda kowa zai gane. DeBarros ya dade yana irin wannan aikin. A yanzu haka shi edita ne na labaran irin wadannan bayanan a Washington, D.C. a jaridar Wall Street Journal (Ana iya saye)

Udemy ya na da darussa kan SQL kyauta a yanar gizo-gizo

Python (wanda ke nufin mesa) shi ne wanda ‘yan jarida su ka fi amfani da shi kuma yana da amfani wajen neman bayanai a shafuka, da tsabtace su da ma yin nazarin su. Ga wasu daga cikin wuraren da za’a iya koyon amfani da python.

A Byte of Python – wannan littafi ne a yanar gizo wanda aka rubuta shi musamman dan koyon python. An rubuta shi ne kuma dan wadanda ba su riga sun lakanci amfani da shi ba yana kuma zuwa da inda za’a iya ajiye abubuwa a shafin GitHub tare da darussan da za’a iya koyo da su.

Shafin datajournalism.com na bayar da darassin gabatarwa dangane da Python wa ‘yan jaridan da ke amfani da Jupyter Notebook. Winny de Jong wata ‘yar jarida a Holland c eke koyar da darussan.

First Python Notebook wannan ma jagora ce ga masu koyon amfani da Python wanda tsohon edita kuma dan jarida da ke aiki da jaridar Los Angeles Times Ben Welsh ya rubuta.

Google’s Python ClassGabatarwa ce kan yadda ake amfani da Python da kuma umurnin yadda za’a iya hadawa a yi amfani da shi.

Learnpython.orgna da darussa a rubuce wadanda za’a iya yi a yanar gizo a shafin da ake kira Python Shell ba tare da an sauke bayanan ba. Batutuwan da ake koyarwa a nan sun fi na google yawa.

Learn Python 3 the Hard Way (2017)wanda Zed Shaw ya rubuta gabatarwa ce ga coding da ke amfani da Python. Idan aka saya kai tsaye daga shafin marubucin, littafin kan zo da bidiyoyin da ke bayani dalla-dalla.

Idan kuna amfani da bayanan da ke hade da yankunan da aka samo su, wadannan shawarwarin za su iya taimakawa wajen yin nazarin bayanan ta yin amfani da taswira.

Fasahohin da aka fi yin amfani da su wajen tsara taswira a dakunan labarai su ne ArcGIS daga Esri (Wanda ke baiwa ‘yan jarida zabin samu kyauta) da kuma budadden shirin QGIS.

Wadansunsu kuma suna da kyau wajen sa hotuna amma sun sanya sashin hotunan taswira daban.

Visualizing Data On Maps Truthfully/ Ganin bayanai a kan taswira cikin gaskiya da aminci

Kasida ce da Inga Schlegel da Johannes Kröger daga jami’ar Hafencity a Hamburg, Jamus suka gabatar a GIJC19.

Datajournalism.com na bayar da darussa ta yin amfani da fasahohin QGIS da CartoDB a karkashin jagorancin Maarten Lambrechts.

JEO wata dabara ce da Gustavo Faleiros ya kirkiro wa shafukan da ke amfani da bayanan da ke dauke da yankunan da su ka fito. Yak an taimakawa kafofin yada labarai da marubutan da ke amfani da taskokin blog da ma kungiyoyi masu zaman kansu wajen wallafa bayanai da taswirorin dijital. Ana iya samun karin taimako a nan/here.

Mapping for Stories: A Computer Assisted Reporting Guide/ Taswira dan labarai: Jagora kan rubuta labarai tare da tallafin komfuta (2017) Wannan littafi ne na koyon amfani da QGIS wajen yin nazarin taswirori kuma yana hade da misalai. Marubutan sun hada da Jennifer Lafleur, David Herzog, Charles Minshew kma suna koya ‘yan jarida masu yin bincike mai zurfi GIS. Da aka fara wallafa littafin an yi shi ne a kan ArcGIs da ESri. (Ana iya saye a shafin IRE)

Mark Monmonnier ya na da litattafai da yawa a kan taswira a ciki har da How to Lie with Maps/ yadda ake karya da taswira wanda aka buga karo na uku yanzu (2018) (Ana iya saye)

R na daya daga cikin fasahohin da aka fi amfani da su wajen tsabtace alkaluma da kuma bayanan da ake sanyawa cikin hoto. Ga wadansu litattafan da za’a iya karantawa dan samun karin bayani. Yawancin wadanda ke da shaguna a yanar gizo an sanya su a karkashin “Training Courses” ko kuma “Darussa” suna bayar da darussan kyauta ko kuma kudin babu yawa.

Datajournalist.com na bayar da gabatarwa ga R a karkashin jagorancin ‘yar jarida kuma bajamushiya Marie-Louise Timcke,

How Do I? / Yaya zan yi? Wannan shafi ne da ke tafiya daura da littafin Sharon Machlis Practical R for Mass Communication and Journalism. Littafin kyauta ne, kuma idan ba’a so a karanta baki daya ana iya binciken batutuwan da ake so sai shafukan su fito,

Intro to R darasi ne daga tsohon dan jaridan Amurka a fannin bayanai Ron Campbell

Practical R for Mass Communication and Journalism (2018) wanda Sharon Machlis ta rubuta. Wannan zai taimaka wa sabon shiga wajen amfani da R a dakunan labarai, tunda yana zuwa ne daga wadda ta dade tana amfani da shi a dakunan labarai. Akwai babi shidda kyauta a intanet.

MaryJo Websters training Materials/Makaman aikin MaryJo Webster Duk wadannan kayayyaki ne da za’a iya amfani da su wajen koyon aikin da farko.

R for Data Science (2016, wanda ke shafukan intanet an sabunta a 2018) wanda Garrett Grolemund da Hadley Wickham suka rubuta na da kayatarwa sosai kuma zai taimakawa duk wanda ke sha’awar amfani da dakin litattafan Tidyverse domin ganin bayanai da ma yin nazarinsu. Wickham kwararre ne kan lambobi da alkaluma wanda kuma dan asalin kasar New Zealand ne amma yana zaune a jami’ar Rice da ke Texas. Grolemund masanin kimiyar bayanai ne kuma babban mai koyarwa na Rstudio. Ana iya sayen littafin amma kuma kyauta ne a intanet.

Wannan shafin na kunshe da kayayyakin horaswa daga dan jaridan Amirka mai amfani da bayanai Andrew Ba Tran. Tran ne kuma ya kirkiro horaswar MOOC Training a R.

Wannan labarin Tiwitan (2019) na dauke da bayanai da yawa dangane da R. Da farko R-Ladies Global ne suka kula da shi, wato kungiyar da ke wakilai a duniya baki daya wadda kuma ke da rajin tabbar da bunkasar jinsi daban-daban a al’ummar masu amfani da R.

Da zarar kun yi nazarin ku wata kila za ku so yin hotuna da taswirorin da za su nuna sakamakon da aka samu, Ga wasu daga cikin wuraren da za’a iya samun hanyoyin inganta labarai.

Chartable – taskar blog ce da aka fara a Jamus a karkashin jagorancin wadanda suka kirkiro manhajan da ke yin hotuna mai suna Datawrapper. Ya na dauke da misalai daga labaran da aka wallafa a kasashen duniya da ma yadda ake abubuwa kamar wannan littafin da Charlotte Rost ta rubuta kan hanyoyin amfani da launi a hotunan bayanai

The Chartmaker Directory wannan jaddawali ne da ke lisafta ire-iren bayanan da ake gani da misalai da kuma irin makaman aikin da ake amfani da su da yadda ake amfani da su.

Data Viz Done Right wannan taskar blog ne da ke nuna misalan yadda hotuna masu inganci kan gyara rahotannin da akan wallafa a duniya baki daya.

The Data Visualisation Catalogue wannan na dauke da ire-iren hanyoyin da za’a iya yin zanen inganta rubutu. Sai dai bayanin shi bai kai na Chartmaker Directory ba

Data Visualization: A Practical Introduction (2018) Wanda Kieran Heady ya rubuta. Wannan littafin na duba shika-shikan samar da bayanai maus inganci da kuma yadda ake amfani da bayanai a R. Healy dan asalin Ireland wanda ke nazarin al’umma da yanayin zamantakewa wanda ke koyarwa a jami’ar Duke. Ana iya sayen littafin a Amazon ko kuma a nan/here

Fundamentaks of Data Visualization (2019) wanda Claus O. Wilke ya rubuta ya yi bayani kan ginshikin data visualization a R kuma ya bayar da fifiko kan irin matsalolin da aka fi fuskanta wadanda yawancinsu kan kai ga bayanan da ke yaudarar jama’a. Wilke jagora ne a sashen nazarin muhallin dana dam da ke jami’ar Texas a Austin. Ana iya sayen littafin a intanet.

Interactive Data Visualization for the Web, 2nd Edition (2017) wanda Scott Murray ya rubuta ya yi bayani dalla-dalla kan amfani da jadawalli ga taswira ta yin amfani da fasahar da ake kira D3 visualization Library. Murray shi ne tsohon mataimakin farfesa a jami’ar San Francisco wanda yanzu yak e aiki da wata kafar yada labarai mai suna O’Reilly Media. (ana iya saye a nan)

Peter Aldhous mazaunin Amurka mai labarai kan kimiyya da kafar yada labaran Buzzfeed yana da shafi da kuma shawarwari da ke taimakawa wajen duba abubuwan da suka shafi R da taswira da nazarin layuka.

PolicyViz taskar blog ce da masanin tattalin arzikin nan dan Amurka Jonathan Schwabish ke kula da shi. Shafin na dauke da misalan irin yadda ya kamata hotunan su kasasnce kuma yana koyarwa a birane daban-daban a Burtaniya da Amurka. (Yana karbar $500 zuwa $800 ko wani zama)

The Truthful Art (2019) wanda Alberto Cairo ya rubuta na bayar da misalai a rubuce da kuma umurnin abubuwan da ‘yan jarida za su iya yi a zahiri. Akwai bayanai kan yadda za’a iya tantance bayanai. Cairo na da babban mukami a irin aikin jaridan da ke amfani da hotuna a jami’ar Miami kuma ya rubuta litattafai da yawa da kuma bidiyoyi da darussa. Ana iya sayen littafin amma kuma akwai shafuka 40 da za’a iya karantawa kyauta. Cairo yana kuma koyarwa a shafin makaranta na Cousera.

VisualizingData.com shafi ne da ke hedikwata a Burtaniya wanda ke da taskokin blog din da be bayar da shawarwari, horaswa a intanet da kuma ido da ido a biranen Manchester da Landan. Yawancin litattafan da rubuce-rubucensa kyauta ne, amma koyarwar kan kai tsakanin $400 zuwa $1,300 kowani zama.

The Visual Display of Quantitative Information (2001) wanda kwararre a illimin statistics ko kuma alkaluma Edward Tufte ya rubuta yana bayar da bayani ne kan yadda za’a iya sanya bayanai a hotuna tare da misalen irin zanen da za’a iya amfani da shi da taswira da kuma hanyoyin kaucewa alkaluman da za su yaudari jama’a. Tufte wanda jaridar New YorK Times ta taba kwatanta shi a matsayin “Da Vinci of Data” wato dai gwarzo a fanin na say a kan bayar da darussa a biranen Amurka da dama inda yak e karbar $380 kowani zama.

Which Chart Could I Use and Why? (2016) Wannan takaitacciyar jagora ce da Peter Aldhous ya rubuta dan bayar da shawara kan jadawali, da launin da suka fi dace wa da ire-iren bayanai.

Visualize This: The Flowing Data Guide to Design, Visualization and Statistics (2011) wanda Nathan Yau ya rubuta na bayar da jagora daki-daki na yadda za’a iya kirkiro hotuna daban-daban idan ana amfani da manhajoji irin su R, Javascript, da PHP. Yau wanda ya yi digirin digirgir a jami’ar UCLA ne ya samar da shafin FlowingData (shafin da ake biya dan samun darussa) sa’annan shi ya rubuta Data Points: Visualization that means something (2013)

Akwai manhajoji da yawa wadanda ake amfani da su wajen ganin bayanai. Wadansu ba su da wahala wajen amfani kuma ba sai an sarrafa su ba, a yayin da wasu kuma su ke da wahalan koyo amma kuma sun fi bayar da irin dabarun da ake bukata. Ga wasu daga cikin wadanda ‘yan jarida su ka fi amfani da su:

ArcGIS wannan daga Esri ne kuma ana amfani da shi wajen raba taswirori a intanet. Yana kuma da ajiya da yawa na taswirorin da ake amfani da su a intanet amma ku tabbata kun yi amfani da wadanda ku ka yarda da sahihancin tushen su. Esri yana da abin da ake kira Storymaps wanda ke taimakawa wajen daidaita labarai da taswirori 

CartoDB ana amfani da shi wajen kirkiro taswira. Akwai na kyauta wa dalibai. ‘Yan jarida kuma na iya biyan $199 kowace shekara dan samun damar amfani da shi a yayin da kungiyoyi kuma za su iya biyan na daidai abin da suke so.

Chartbuilder – Wannan manhajan na kyauta ne. Ba shi da abubuwa da yawa amma dai zai taimaka da tura hotuna zuwa manhajoji irin su SVG ko JSON

D3 kamar dakin ajiya da kirkiro bayanai ne na Javascript. Ana iya yin zane da shi. Akwai misalan ire-iren abubuwan da ake iya zanawa a nan/here. Akwai kuma darasi na bidiyo da za’a iya gani a nan/here. Duk abubuwan da ya kamata a karanta an fassara su zuwa harsuna daban-daban wadanda suka hada da Chinese, Spanianci, Rashanci, Harshen Turkiyya da Portuganci.

Datawrapper wannan a Jamus aka krikiro kuma bay a bukatar wani kwarewa na musamman. Ana iya zane iri-iri har ma da taswira. Akwai na kyauta amma ba zai bayar da abubuwa masu amfani da yaw aba. Na kudin kuma akwai farashi daban-daban. Akwai na dalibai, na mutun daya ko kuma kungiya sa’annan da dakunan labarai. Farashin ya kama daga $33 a wata zuwa $564 a wata. Ana iya samun bayanai a shafin kyauta kuma akwai darussa a rubuce a shafin Academy

Plotly Chart Studio shafi ne da ke taimakwa wajen zane da taswira da jadawali cikin sauki. Shi ma ana biya daga $99 a shekara wa dalibai zuwa $840 a shekara wa ma’aikata

Plotly.js na kyauta ne kuma ana iya amfani da shi wajen yin JavaScript. Yana bukatar ilimin programming. Akwai sigogi daban-daban a R, Python da sauran harsunan fasahar. Akwai rubuce-rubuce a kan shi a GitHub

StoryMapJS manhaja na kyauta ne wanda ke taimakawa wajen rubuta labarai a intanet da ke bayyana wuraren da abubuwa suka faru. Sabon manhaja ne amma kuma bas hi da matsala kuma kusan kowa na iya amfani da shi

Tableau shi ma yana yin duk hotuna da zane-zanen. Ana iya duba shafin domin ganin farashi. Kyauta ne ga mambobin Investigative Reporters and Editors. Tableau Public kyauta ne sai dai shi kuma ba shi da armashin da sauran ke da shi.

Timeline JS shi ma kyauta ne kuma yana taimakawa wajen yin duk zanen da ake bukata musamman irin wanda za’a iya latsawa a ga abin da ake so a gani. Akwai shi a harsuna 40. Bayanan na kan manhajan lissafin google ko kuma google spreadsheet dan haka babu wahalan kara bayanai ko sabunta shafin.

 

Muna maraba da shawarwari dan inganta batutuwan da ke shafinmu. Kuna iya rubuto mana a nan.

Godiya: Ma’aikatan GIJN suka shirya wannan tare da hadin gwiwan taron karawa juna sani na masu dauko rahotannin da ke bincike mai zurfi da ke makarantar sadarwa a jami’ar Amurka, tare da gudunmawa daga Helena Bengsston, John Bones, Fred Vallance Jones, Madeleine Davison, Flor Coelho, Jennifer LaFleur da Brant Houston.

English Version

Our Partners
Bill and Melinda Gates Foundation
British_Council_logo
EuropeanUnion
Ford-Foundation-Logo
FPressUnlimited
gijn
HBS
Luminate
macarthur
nrgi
NED Logo
osiwa
PTLogo
ppdc

Previous
Next